Girke-girken Ramadan: Yadda ake gasa naman rago

Bayanan bidiyo, Girke-girken Azumi
Girke-girken Ramadan: Yadda ake gasa naman rago
An wallafa

Wannan wani shiri ne da BBC Hausa take kawo muku kullum a cikin watan azumi don bai wa mata damar gwangwaje basirarsu ta girki.

A wannan bidiyo, za ku kalli gwanar girkin tamu ta yau, tana nuna mana yadda ake gasa naman rago.

Raƙayya Suleiman wadda aka fi sani da homeofdelicious a shafukan sada zumunta, gwanar mai girki ce kuma ta nuna mana kayan haɗin gasasshen rago mai tada kwaɗayi.