Arsenal ta ci gaba da zama ta daya a Premier League

An wallafa

Arsenal ta je ta doke Tottenham 3-2 a wasan mako na 35 a gasar Premier da suka kara a wasan hamayya ranar Lahadi.

Gunners ta fara zura kwallo a raga ta hannun Pierre-Emile Hojbjerg, wanda ya ci gida a minti na 15 da fara wasa.

Kwallo na biyar kenan a wasan hamayya na kungiyoyin Arewacin Landan da Tottenham kan ci gida, inda Arsenal kan fara yin gaba a wasa da cin 1-0.

Wadanda suka ci gida a baya a Tottenham a gasar Premier League sun hada da

Armstrong a Maris din 2000 da Wimmer a Nuwambar 2016 da Lloris a Janairun 2023 da Romero a Satumbar 2023 da wadda Hojbjerg ya ci gida a wasan Lahadi.

Arsenal ta zura kwallo na biyu ta hannun Bukayo Saka a minti na 27, kuma na 15 da ya zura a raga a Premier League a kakar nan.

Haka kuma Saka ya zama dan wasan tawagar Ingila da ya ci Tottenham gida da waje a Premier League a kaka daya, tun bayan bajintar Ian Wright 1993/94.

Saura minti bakwai su je hutu ne Arsenal ta kara ta uku ta hannun Kai Havertz.

Daga baya ne Tottenham ta zare biyu ta hannun Cristian Romero da Heung-min Son a bugun fenariti.

Karo biyu a jere Arsenal na zuwa ta na cin Tottenham tun bayan Satumbar 1988 da ta yi nasara uku, karkashin George Graham.

Kafin nan wasa biyu Gunners ta ci a gidan Tottenham daga fafatawa 17 da ta kai ziyara a Premier da canjaras shida aka doke ta tara daga ciki.

Mikel Arteta ya ci wasa na 100 a Premier League a Arsenal:

Wannan shi ne wasa na 100 da Mikel Arteta ya ci a Premier League a karawa ta 169 da ya ja ragamar Arsenal a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Cikin wasannin ya yi canjaras 27 aka doke shi 42 da cin kwallo 321, aka zura wa Gunners 179.

Bayan da Gunners ta doke Tottenham ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin Premier League da maki 80, yayin da Manchester City ce ta biyu mai maki 79, mai kwantan wasa daya.

Liverpool, wadda ta tashi 2-2 da West Ham United tana ta ukun teburi da maki 75.

Wasannin dake gaban Manchester City da na Arsenal:

Man City: 4 Mayu a gida da Wolves; 11 Mayu zuwa gidan Fulham; 14 Mayu zuwa gidan Tottenham; 19 Mayu a gida da West Ham.

Arsenal: 4 Mayu a gida da Bournemouth; 12 Mayu zuwa gidan Man Utd; 19 Mayu a gida da Everton.