Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tsofaffin mutane na zanga-zanga a China kan rage musu tallafin kiwon lafiya
Dandazon mutanen da suka ritaya a China sun sake fitowa kan tituna domin yin zanga-zanga kan rage musu tallafi da aka yi a bangaren kiwon lafiya.
Sun taru a karo na biyu a birnin Wuhan ranar Laraba, inda aka fara samu bullar cutar korona, wurin kuma da ke arewa maso gabashin birnin Dalian.
Zanga-zanga ta biyu cikin kwanaki bakwai na ƙara matsin lamba kan gwamnatin shugaba Xi Jinping makonni kalilan kafin gudanar da babban taron jam'iyyar National People Congress, inda za a zaɓi sabbin shugabanni.
An fara samun zanga-zanga ne a Wuhan a ranar 8 ga watan Febrairu bayan da hukumomin larduna suka ce za su zabtare tallafin bangaren lafiya wanda yana cikin alfanu da mutanen da suka yi ritaya ke samu daga wajen gwamnati.
Hotuna daga kafafen sada zumunta sun nuna masu zanga-zanga wadanda yawanci tsofaffi ne, suna cewa rage tallafin ya zo musu ne a daidai lokacin da kiwon lafiya ke ƙara tsada.
Duk da cewa shugabannin larduna ne ke lura da irin waɗannan tsare-tsaren inshorar lafiya, zanga-zangar ta yaɗu zuwa sassan ƙasar da dama, wanda ya sake nuna yakinin da mutane ke da shi ko na karfin yin zanga-zanga a China.
A karshen shekarar da ta wuce, dubban matasa a China, sun shiga zanga-zangar da ta tilsata wa gwamnati sake duba matakai kan cutar korona – mutane sun gaji da ci gaba da yin gwaje-gwajen cutar da sanya dokar kulle, abin da ya sanya tattalin arzikin ƙasar shiga cikin barazanar taɓarɓarewa.
Sai dai, sauya tsari nan take ya sanya tsarin kiwon lafiyar China cikin wani hali, yayin da cutar korona ke ci gaba da yaɗuwa a sassan ƙasar da dama.
Hakan ya janyo rashin sanin ainihin alkaluman mutanen da suka mutu, inda wani rahoton BBC ya nuna cewa yawancin waɗanda suka mutu tsofaffi ne.
Rage tallafin bangaren lafiya ga waɗanda suka yi ritaya, wanda hukumomi suka kwatanta a matsayin sabbin sauye-sauye, na zuwa ne a daidai lokacin da China ke farfadowa daga bala’in annobar korona.
Hukumomi sun ce an yi tsarin ne da nufin sake inganta yanayin wasu yankuna.
Sai dai, mutane sun yi ta suka a kafafen sada zumunta, inda suka ce hukumomin ƙasar na koƙarin ɗeɓe ɗimbin kuɗaɗe da aka yi amfani da su wajen tilasata gwajin cutar korona da kuma wasu matakai da aka ɗauka.
Hukumomi a Wuhan da Dalian sun ce ba su da masaniyar zanga-zangar da ake yi a baya-bayan nan, don haka, ba za su ce komai ba. Haka na ba a amsa kiran waya da aka yi wa ofisoshin ‘yan sanda ba.
Wani gidan redio ya ruwaito cewa waɗanda suka yi ritayan a bangaren sarrafa tama da ƙarafa ne suka fi yawa a zanga-zangar da aka yi a Wuhan.
Ci gaba da amfani da kafafen sada zumunta zai taimaka wajen bayyana yadda ake tsara haɗuwar dandazon mutane a faɗin ƙasar, inda shirya zanga-zanga kan gwamnati ta kowane bangare ke da wahala da kuma kan iya janyo hukunci mai tsanani, wanda ya haɗa da ɗauri a gidan yari.
Hotunan bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta sun nuna tsofaffin mutane a filin zaga-zangar na rera taken jam’iyyar kwamunisanci.
A baya, rera wannan waka na nufin masu zanga-zanga na goyon bayan gwamnati ko kuma jam’iyyar ta kwamunisanci, amma suna son a biya musu hakkokinsu.
Wani mai shago da ya kalli yadda zanga-zangar ta gudana a Wuhan a ranar Laraba, ya faɗa wa BBC cewa ‘yan sanda sun toshe kowane bangare na hanyoyin da ke kaiwa yankin domin hana ƙarin mutane shiga zanga-zangar da ɗaruruwan tsofaffin ke yi tare da rera wakoki.
Shekara uku bayan ɓarkewar annobar korona da kuma sake dawo da matakan cutar a wasu wurare, ya janyo fushi kan tsare-tsaren kiwon lafiyar China daga wajen ‘yan ƙasar.
Mista Xi Jinping, ya amince da tsare-tsaren cutar korona da aka saka sannan jam’iyyarsa ta gaza fitowa ta yi magana kan sake dawo da wasu matakai nan take.
Gwamnatin China ta kuma fito fili ta soki wasu ƙasashe saboda buɗe iyakokinsu da sauri, inda ta ce sun sadaukar da mutanensu a kan duk abin da zai faru da su.
Sai dai, Chinan ta dawo ta yi watsi da nata matakan cikin sauri fiye da kowace ƙasa, inda suka yi hakan bayan saka dokar kulle da wasu tsare-tsare masu tsauri na dogon lokaci fiye da ko’ina a duniya.
Yanzu, yawancin mutane a nan, na da yakinin cewa sakamakon tsare-tsaren gwamnati, an rasa rayuka da dama.
A shafin sada zumunta na kafar Weibo da ke China, an yi ta amfani da maudu’in inshorar lafiya a faɗin China – wanda kuma ya janyo hankalin miliyoyin mutane, amma daga baya kafar ta cire shi daga manyan labaranta.
Maudu’in ya tattaro mutane da dama da suka yi zanga-zanga a Wuhan – a dandalin Zhongshan – inda aka cire wasu hotuna da aka ɗauka daga zanga-zangar a kan kafofin sada zumunta.
Sai dai, duk da irin matakai da China ke ɗauka na ganin sai abin da take so ake wallafawa, ana ci gaba da nuna goyon baya ga masu zaga-zangar waɗanda yawancinsu suka yi ritaya a kafafen sada zumunta.
Beijing na buƙatar samo hanyar da za ta warware wannan lamari, muddin tana son ƙauce wa ƙaruwar masu bore a ƙasar.