Amfanin tazargaje a jikin ɗan'adam

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Amfanin tazargaje a jikin ɗan'adam
An wallafa

Yayin da mutane da dama a Najeriya ke fama da zazzaɓin cutar Maleriya kasancewar lokacin damina, likitocin gargajiya na shawartar mutane wajen amfani da tazargade.

BBC ta tattauna da Dakta Zainab Ujudu Shariff wata mai haɗa maganin gargajiya a ƙasar inda ta yi bayanin hanyar gargajiya ta amfani da tazargade wajen magance cutar Maleriya.

An amfani da tazargade wajen magance cututuka masu yawa.

Zainab ta ce a kimiyance ana amfani da sinadarin tazargade wajen haɗa maganin Maleriya na Bature.

"WHO ta ce duk itace da aka saba ana amfani da shi tsawon shekara 200,000 to a yadda yana magani", in ji Zainab.

Ta ƙara da cewa baya ga Maleriya akwai cututuka masu yawa da tazargade ke warkarwa.