Yawaitar shan shisha a tsakanin ‘yan mata
'Yan mata matasa, musamman dalibai da ke makarantun sakandare da jami'oi na daga cikin masu wannan al'adar.
Ko da yake wasu shan tabar a gidajensu, yawaitar wuraren shan wannan taba na kara yawa a wasu biranen kasar.
Yayin da ake fito da wasu nau'ukan shisha na lataroni da ake iya ajiya a jaka kuma a yi yawo da shi.
Hukumar yaki da cututtuka ta Amurka, CDC, ta ce binciken da aka yi a kan shisha mai sinadarin tobacco da na gargajiya sun nuna cewa duka suna kunshe da gurbataccen iskar carbon monoxide, da wasu abubuwa masu guba da ke kara hadarin kamuwa da cutar kansa da ciwon zuciya da na huhu.
Sinadarin tobacco da ake amfani da shi a shishan da kuma hayakin da tabar ke fitarwa na dauke da abubuwa masu guba da ke janyo sankarar huhu da ta mafitsara da kuma ta baki.
Hukumar ta kuma kwatanta illolin shisha da ta taba sigari, inda ta ce bincike-binciken da aka yi sun nuna cewa hayakin shisha na dauke da sinadaran nicotine da tar da kuma karafa masu yawa.
Shafe sa'a guda ana shan shisha tamkar shan hayakin sigari 100 ne zuwa 200. Yayin da a zaman shan tukunyar shisha, mutane ke fuskantar hadarin shakar gurbatacciyar iskar carbon monoxide da kuma kashi daya da digo bakwai na sinadarin nicotine da ake samu a karan sigari guda.
Haka zalika hayakin da mutane ke shaka, a wannan zama ya kai mililita 90,000 idan aka kwatanta da 500 zuwa 600 da ake shaka a sigari guda.