Mata da mijin da suka yi fice a waƙoƙin Annabi tare

Bayanan bidiyo, Danna hoton sama ku kalli bidiyon:
Mata da mijin da suka yi fice a waƙoƙin Annabi tare
An wallafa

Duk da tarin mawaƙan yabon Manzon Allah Annabi Muhammadu S.A.W. da ake da su a ƙasar Hausa da duniya baki ɗaya, ba kasafai ake samun mata da miji na yin yabon a tare ba.

Wannan ta sa Hafiz Abdallah da matarsa Murja Bukhari Adam - wadda wasu ke kira da sunan mijinta - suka yi fice a fagen waƙoƙin yabon Annabi.

Ma'auratan, waɗanda 'yan asalin Jihar Kano ne, malami ne da ɗalibarsa kafin su yi aure.

"Ni ɗalibarsa ce, tun a Islamiyya yake ban ƙasidu kuma da Allah ya tashi ikonsa sai ya haɗa wani abu mai girma - shi ne aure," kamar yadda Murja ta shaida wa BBC Hausa game da mijinta.