Ku San Malamanku tare da Farfesa Abubakar Abubakar Yagawal

Bayanan bidiyo,
Ku San Malamanku tare da Farfesa Abubakar Abubakar Yagawal
An wallafa

A wannan mako cikin shirin Ku San Malamanku, mun kawo muku tattaunawa da Farfesa Abubakar Abubakar Yagawal, malamin addinin Musulunci a jihar Sokoto.

An haifi malamin a 1956 cikin kauyen Yagawal na karamar hukumar Tambuwal. Kuma ya fara karatun addinin Musulunci a Hizbur Raheem Talamilatus Sheikh Ibrahim.

Daga nan kuma ya tafi makarantar Sultan Abubakar College, Sokoto, kafin ya zarce Kwalejin Ilmi ta Sokoto don karatun shaidar malanta.

Ya yi digirinsa na farko a fannin Larabci cikin Jami'ar Usman Danfodio, daga nan kuma ya tafi Jami'ar Bayero Kano, inda ya yi digirinsa na biyu.

Cikin fitattun malaman da suka yi tasiri a rayuwar Farfesa Abubakar Yagawal akwai Shehi Muhammadu Moyi Tambuwal da Mallam Amadu Jega Mallam Ibrahim Tambuwal.