Casemiro ba zai buga wa United wasan Newcastle ba

An wallafa

Manchester United za ta ziyarci Newcastle United ranar Lahadi, domin buga wasan Premier League mako na 29.

To sai dai Casemiro ba zai yi mata wasan ba, wanda aka dakatar karawa hudu, bayan jan kati da aka yi masa.

An bashi jan kati a wasa da Southampton da suka tashi 0-0 a Old Trafford, inda Anthony Taylor ya kore shi, bayan karbar katin gargadi biyu.

Tun kan nan an kore shi a gasar Premier karo biyu a bana a fafatawa da Crystal Palace ranar 4 ga watan Fabrairu a Old Trafford.

Bai buga wasan da United ta ci Fulham 3-1 a FA Cup ba, ba zai yi fafatawar Premier da Newcastle da Brentford da kuma Everton ba nan gaba.

Wasan farko da United za ta buga kenan, bayan da aka kammala wasannin da Fifa ta ware da suka shafi na shiga Euro 2024 da na kofin Afirka da na sada zumunta.

Kungiyoyin biyun sun tashi 0-0 a Old Trafford a Premier League ranar 16 ga watan Oktoban 2022, sannan United ta ci 2-0 ta lashe Carabao Cup ranar 16 ga watan Fabrairun 2023 a Wembley.

United tana mataki na uku da maki 50 a teburin Premier, ita kuwa Newcastle tana ta biyar mai maki 47, bayan da suka yi karawa 26 kowacce.

Marcus Rashford ya fara atisaye, bayan raunin da ya ji a wasan Fulham a FA Cup, wanda bai yi wa Ingila wasa da Italiya da Ukraine ba.

Tawagar Ingila ta doke ta Italiya 2-1, sannan ta ci Ukraine 2-0 a wasan neman shiga gasar kofin nahiyar Turai da za a yi a Jamus a 2024.

Da kyar idan Marcel Sabitzer zai yi wa United karawar, wanda ya ji rauni a lokacin da yake buga wa Austria wasa - bai kuma fuskanci Estonia ba a Euro 2024.

Ana sa ran Erik ten Hag zai yi karin bayani kan koshin lafiyar Marcel.

Zai kuma sanar da halin da Anthony Martial da Raphael Varane ke ciki– wadanda ba su buga FA Cup ba a wasa da Fulham.

Ranar Juma'a kociyan United zai gana da 'yan jarida, don fayyace halin da kungiyar ke ciki a shirin zuwa St James Park.

Wadanda ke jinya a United sun hada da Christian Eriksen da Donny van de Beek da kuma Alejandro Garnacho.

A bangaren Newcastle kuwa, Joelinton zai koma buga tamaula, bayan da aka dakatar da shi karawa biyu.

Sven Botman ya koma atisaye a makon nan, wanda bai yi wa Netherlands wasan neman shiga Euro 2024 ba, sakamakon rashin lafiya.

Miguel Almiron ba zai iya buga fafatawar ba har da mai tsaron baya, Emil Krafth, ana tantama kan koshin lafiyar Anthony Gordon da Allan Saint-Maximin da kuma Nick Pope.

Manchester United, wadda ta lashe Carabao Cup a bana ta kai quarter finals a Europa League, za ta fuskanci Sevilla gida da waje.

Haka kuma ta kai zagayen daf da karshe a FA Cup, wadda za ta kece raini da Brighton a Wembley.

Bayan rashin nasara da Newcastle ta yi a hannun United a Wembley, Manchester City ta doke ta 2-0 a Premier, sai dai ta yi nasara a kan Wolves da Nottingham Forest.

Raflin da zai busa wasan da mataimakansa:

Rafli: Stuart Attwell. Mai kula da VAR Andy Madley da Michael Salisbury, mai jiran ko-ta-kwana.

Wasannin mako na 29 da za a kara:

Asabar 1 ga watan Afirilu

  • Manchester City da Liverpool
  • Bournemouth da Fulham
  • Nottingham Forest da Wolves
  • Crystal Palace da Leicester
  • Arsenal da Leeds
  • Brighton da Brentford
  • Chelsea da Aston Villa

Lahadi 2 ga watan Afirilu

  • West Ham da Southampton
  • Newcastle da Manchester United

Litinin 3 ga watan Afirilu

  • Everton da Tottenahm