Bakanon da ke yi wa mata kitso a Abuja
A wani lamari da ba a saba gani ba, wani matashi da ya kammala digirinsa ya samu sana’a ta yi wa mata kitso a Abuja, babban birnin Najeriya.
Muhammad Yusuf mai shekara 35 ya ce yana yin kitson ne don yana da sha’awar hakan kuma ya samu karbuwa a wajen mata.
Ya fara sha’awar sana’ar ne a lokacin da yake sayar da gurguru inda yake tsayawa a gaban shagon gyaran gashi na mata yana kallon yadda ake aikin.
Wata rana sai mai shagon ta gayyace shi ya fara gwaji, daga haka har ya ƙware.
A yanzu ya zama abin koyi ga dumbin matasan da ba su da aikin yi, da nuna musu cewa ba sai sun jira aikin ofis mai gwabi ba kafin su samu rufin asiri.
Sai dai Muhammad dan asalin jihar Kano, ya ce matsalarsa daya ce, yadda matarsa ke damuwa da nuna kishi kan matan da yake yi wa kitson.



