De Bruyne ya buga wa Man City wasa a karon farkon tun bayan Agusta

An wallafa

Manchester City ta kai zagaye na huɗu a FA Cup, bayan da ta doke Huddersfield Town 5-0 a Etihad ranar Lahadi.

Kevin de Bruyne ya buga fafatawar a karon farko tun bayan jinya daga watan Agustan shekarar bara.

De Bruyne ya shiga wasan a zagaye na biyu, inda Man City mai rike da FA Cup ta ci kwallo biyu ta hannun Phil Foden da Julian Alvarez da Jeremy Doku da kuma Ben Jackson da ya ci gida.

Manchester City ce ta lashe kofin bara, wadda ta haɗa har da na Premier League da kuma Champions League.

City ta zama ta farko a Ingila da ta lashe kofi biyar a shekara ɗaya, wadda ta ɗauki Uefa Super Cup da kuma Fifa World Club Cup.

Magoya bayan Man City sun yi ta cewa suna buƙatar a ci kwallo 10 a ranar Lahadi - kamar yadda ta yi wannan kwazon na zura kwallo 10-1 a ragar Huddersfield a 1987.

Manchester City tana mataki na uku a teburin Premier League da maki 40 iri ɗaya da na Arsenal ta huɗu.

Liverpool ce ke kan gaba a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 45 da kuma Aston Villa ta biyu da tazarar maki uku tsakaninta da ƙungiyar Anfield.