An tuhumi Manchester City da kasa tsawatarwa 'yan wasanta

An wallafa

An tuhumi Manchester City da laifin kasa tsawatarwa 'yan wasanta a wasan da ta tashi 3-3 da Tottenham a gasar Premier League ranar Lahadi.

'Yan wasan City sun mamaye alkalin wasa, Simon Hooper, wanda ya bayar da bugun tazara daf da za a tashi a lokacin da kwallo ya je wajen Jack Grealish bayan da ya nufi raga.

Tun farko Hooper bai busa ketar da aka yi wa Erling Haaland ba, amma kwallo na zuwa wajen dan wasan tawagar Ingila sai kawai ya busa usur.

An bai wa City nan da ranar Alhamis 7 ga watan Disamba domin ta kare kanta daga tuhumar da ake yi mata.

Haaland yana daga cikin 'yan wasan City da suka fi korafi a fafatawar, har ma ya caccaki alkalin wasan a dandalin sada zumunta na X.

Wasa na uku kenan da City ta yi canjaras a Premier League a jere, bayan 4-4 da Chelsea, da kuma 1-1 da Liverpool.

Hakan ne ya sa City ta koma ta ukun teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 30, da kuma tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool.

Arsenal ce ta daya a kan teburin Premier League da maki 33, bayan da aka kammala wasannin mako na 14.