Ku San Malamanku tare da Sheikh Ali Muhammad Al Ahmar

Ku San Malamanku tare da Sheikh Ali Muhammad Al Ahmar
An wallafa

Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya yi hira ne da Sheikh Ali Muhammad Muhammad Al Ahmar, wani fitaccen malami a jihar Borno.

An haifi malamin ne a garin Maiduguri a watan janairun 1976.

Ya fara karatunsa a makarantar allo tare da Sayyada Aisha inda daga baya ya koma tsangayar Gwani Umar Musa.

Bayan nan sai ya koma tsangayar Gwani Jidda Jibril inda ya haddace kur’ani.

Ya kuma yi karatu a wajen Sayyadina Hassan Almuqri wanda ya je Najeriya daga Chadi.

Ya yi ruwaya hudu ta karatun Kur'ani tare da malamin, ciki har da Hafs da Warsh da Madani da ruwayar Abu Amr Al Basr.

Malam ya kuma yi karatun boko a makarantar firamare ta Annahda Al-Islamiyya ta Sheikh Sharif Saleh daga shekarar 1983 zuwa 1988.

Ya yi karatun sakandire a Kwalejin Elkanemi.

Bayan ya kammala ne sai ya samu tafiya yin karatun digiri a wata Jami'a a Libiya, wato College of Islamic Call a 1988.

Ya yi digirin farko da na biyu har da digirin-digirgir a can, inda ya zama ɗan Najeriya na farko da ya yi karatu har zuwa wannan matakin a Libiya.

Ku kalli bidiyon don jin cikakkiyar hira kan al'amuran rayuwar malam.