Shirin da muke yi na ƙwace mulki daga hannun APC - Ahmed Makarfi
Shirin da muke yi na ƙwace mulki daga hannun APC - Ahmed Makarfi
An wallafa
Shirin Gane Mini Hanya na wannan makon ya tattauna da tsohon Gwamnan Kaduna Ahmed Makarfi kuma tsohon shugaban jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya.
A Najeriya, wasu daga cikin shugabannin babbar Jam'iyyar adawa ta PDP sun jaddada bukatar hadin kai da sauran jam'iyyun adawa na kasar, don iya karbe mulki cikin sauki a hannun jam'iyyar APC mai mulki.
A tattaunawarsu da Yusuf Tijjani, Tsohon gwamnan jihar Kaduna Sanata Ahmed Makarfi, wanda ya taba rike mukamin shugabancin jam'iyyar PDPn, ya yi tsokaci game da muhimman batutuwan da suka shafi jam'iyyar da babban zaben 2023.