Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
PSG ta ɗauki Milan Skriniar daga Inter
Paris St-Germain ta ɗauki ɗan wasan baya Milan Skriniar daga Inter Milan kan kwantaragin shekara biyar.
Ɗan wasan Slovakia ya yi wa Inter Milan wasa na tsawon shekara biyar kuma ya lashe Serie A a kakar 2020-2021.
Dan wasan me shekara 28 wanda kwantaraginsa ta ƙare da Inter, ya sanya hannu ne kwana guda bayan PSG ta sanar da ɗaukar sabon kocinta Luis Enrique.
"PSG na ɗaya daga cikin ƙungiyoyi masu ƙarfi a duniya tana da 'yan wasan a gani a faɗa ga kuma magoya baya masu abin mamaki," Skriniar.
"Zan yi farin cikin kwallo a wannan ƙungiya."
An ta raɗe-raɗin ɗan wasan zai koma gasar Premier, yayin da aka ce Tottenham da Liverpool na neman shi.