Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid ka iya ɗaukar Haaland da Mbappe, Man United na son Neto
Real Madrid ta yi shirin fito da kuɗi a kakar baɗi bayan kyalla idonta da ta yi kan ɗan wasan PSG da Faransa Kylian Mbappe mai shekara 24, da kuma na Norway da Manchester City Erling Haaland mai shekara 23. (AS - in Spanish)
Dan wasan bayan Chelsea Ian Maatsen mai shekara 21 zai iya komawa Manchester City, bayan City ta fara ƙulla alaƙa da ɗan wasan Netherlands din. (Football Insider)
Arsenal za ta yi watsi da duk tayin da aka yi mata kan ɗan wasanta na Japan Takehiro Tomiyasu ɗan shekara 25, yayin da Bayern Munich ta nuna sha'awarta a kan shi. (Standard)
Mancheter United da Arsenal da wasu ƙungiyoyi masu dama daga Saudiyya na nuna kwaɗayinsu kan ɗan wasan Portugal Neto Pedro mai shekara 23, sai dai Wolves ba za ta ƙarbi duk wani abu da ya yi ƙasa da fan miliyan 60 ba.(Teamtalk)
Manchester united na neman yadda za ta ƙara ƙarfafa bayanta, ta hanyar ɗako ɗan wasan kungiyar Nice ta Faransa Jean-Clair Todibo mai shekara 23, da ɗan bayan Sporting Lisbon Goncalo Inacio mai shekara 22, a wani mataki na maye gurbin tsohon ɗan wasan Faransa Raphael Varane ɗan shekara 30. (Sun)
Dan wasan tsakiya na Manchester United da Brazil Casemiro mai shekara 31 zai iya barin ƙungiyar a watan Janairu yayin da United ɗin ke neman yadda za ta sake kyakkyawan zubi na yan wasanta. (Teamtalk)
Chelsea na ci gaba da tuntuɓa kan ɗan wasan Palmeira da Brazil Estovao Willian mai shekara 16, wanda ake cewa sai an biya fan miliyan 52 kuɗin barinsa ƙungiyar. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Newcastle da Wolves za su fafata wajen ɗaukar ɗan bayan Senegal Arounda Sangate mai shekara 21. (Football Insider)
Barcelona ta ƙagu ta ɗauki ɗan wasan Tottenham da Argentina Giovani Lo Selso mai shakara 27 yayin da take neman wanda za ta maye gurbin Gavi da shi wanda ya ji rauni. (Mundo Deportivo - in Spanish)