Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Sheikh Imam Mansur
Ku San Malamanku tare da Sheikh Imam Mansur
An wallafa
Cikin shirin Ku San Malamanku na wannan mako BBC ta tattauna da Sheikh Ibrahim Mansur, wanda aka fi sani da Shehu Mansu.
Shehu Mansur ya ce ya fara karatu ne a gaban mahaifinsa kamar ko wanne Malami.
Gabansa ya fara karatu shi ya koya masa Jauhara da Salatul Fatihi da sauransu gabanin ya kai shi makarantar Madinatul Ahbab ta Shehu Haruna Rasheed.
A wannan makarantar ya yi saukar Al-Ƙur'ani a 1987 kafin daga bisanin a 1992 ya yi hadda duka dai a makarantar