West Ham ta dauki aron Phillips daga Man City zuwa karshen kaka

An wallafa

West Ham ta kulla yarjejeniyar da Manchester City don daukar aron Kalvin Phillips zuwa karshen kakar bana.

Phillips, mai shekara 28, ya saka hannu kan kunshin kwantiragin kaka shida lokacin da ya koma Ettihad daga Leeds kan £45m a Yulin 2022.

To sai dai ba ya samun buga wasanni sosai karkashin Pep Guardiola, wanda ya buga karawa biyu kacal a bana.

Phillips, wanda Juventus ke son dauka, na daf da zuwa West Ham a makon nan domin a auna koshin lafiyarsa.

West Ham ce za ta dinga biyan albashin ɗan kwallon, haka kuma za ta iya mallakar Philips a karshen kakar nan, idan ya taka rawar gani.

Kungiyoyi da dama sun yi sha'awar daukar Philips, amma City ta bukaci kudi mai yawa kafin ta amince ta bayar da aronsa.

Phillips, wanda mamba ne a tawagar Ingila da Gareth Southgate ke jan ragama, zai koma Ingila ranar Talata tare da ƴan wasan City daga ɗan atisayen da kungiyar ta yi a Abu Dhabi.

Daukar Philips da West Ham za ta yi zai taimaka wa kungiyar, bayan da koci, David Moyes ke kokarin kara karfin kungiyar mai fama da ƴan wasa da ke jinya.

Shi kuwa Philips na hangen wannan lamarin a matakin damar da zai kara nuna kansa a fannin tamaula.