Yadda aka ceto masu haƙar ma'adanan da ƙasa ta rufta musu

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Yadda aka ceto masu haƙar ma'adanan da ƙasa ta rufta musu
An wallafa

Bayan ruwan sama mai ƙarfi, wasu masu haƙar ma'adanai sun tsallake rijiya da baya a wani wurin haƙar ma'adanai na Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo.

Wani mutum ne ya yi amfani da hannunsa wajen zaƙulo mutanen daga cikin rami.

Wannan bidiyon ya nuna yadda mutanen ke ɓulɓulowa ta wata ƙaramar kafa yayin da mutane ke ƙoƙarin kawar da ƙasar da ta toshe.