Newcastle na son aron Kalvin Philips, Ancelotti ka iya ci gaba da zama a Madrid

An wallafa

Newcastle za ta nemi aron ɗan wasan Manchester City da Ingila mai shekara 27, Kalvin Philips da kuma ɗan gaban PSG Hugo Ekitike mai shekara 21 a watan Janairu.(Times - subscription required)

Kungiyar da Eddie Howe ke jagoranta na da muradin ɗan wasan Stuttgart da Guinea Serhou Guirassy ɗan shekara 27 da kuma ɗan wasan Everton Dominic Calvert-Lewin mai shekara 26. (Teamtalk)

Brentford ba ta da shirin sayar da ɗan wasanta ɗan Ingila Ivan Toney mai shekara 27, duk da sha'awar da Arsenal da Chelsea ke nuna wa kan sa.(Mirror)

Manchester United ta sanya ɗan wasan Ingila da Everton Jarrad Branthwaite mai shekara 21 a matsayin ɗan bayan da take son ɗauka a 2024. (Teamtalk)

Kungiyoyin Saudiyya na shirin bayar da fan miliyan 17 a matsayin kuɗin sayan dan wasan Manchester United da Denmark da Christian Eriksen ɗan shekara 31 nan da watan Janairu. (Caught Offside)

Real Madrid na shirin bai wa Carlo Ancelotti mai shekara 64 damar tsawaita kwataraginsa a ƙungiyar duk da cewa Brazil na da shirin ɗaukar shi. (90min)

Kocin Barcelona Xavi ya musanta jita-jitar cewa dan wasan Jamus Ilkay Gundogan mai shekara 33, zai bar ƙungiyar zuwa Saudiyya a watan Janairu. (Goal.com)

Bayern Munich ta shiga gaban Manchester United da Chelsea wajen shirin ɗaukar ɗan wasan Jamus da Schalke Assan Ouedraogo mai shekara 17.(Teamtalk)

AC Milan na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan Brazil da Manchester City Yan Cout mai shekara 21 da ke zaman aro a Girona da ke La Liga. (Calciomercato)

Ana sa ran ɗan wasan Argentina Lautaro Martinez mai shekara 26 zai tsawaita kwataraginsa a Inter Milan, bayan ya yi watsi da tayin da ya samu daga kungiyoyin Saudiyya a bara. (Tuttosport via Football Italia)