An ci tarar Man United da Crystal Palace kowacce fam 55,000

An wallafa

An ci tarar Manchester United da Crystal Palace fam 55,000 kowacce.

An samu kungiyoyin da laifin kasa tsawatarwa 'yan wasansu a Premier League a Old Trafford a watan nan.

An bai wa dan wasan United, Casemiro jan kati, sakamakon shake wuyan Will Hughes, bayan wata takaddama da ta barke a zagaye na biyu a karawar.

Hatsaniyar ta barke bayan da dan kwallon Palace, Jeffrey Schlupp ya bangaje dan wasan United, Antony a gefen fili, dukkansu an ba su katin gargadi.

United ta amince da cin tarar, bayan da Palace ta ce ba laifinta bane.

Wani kwamiti ne mai zaman kansa ya tukumi kungiyoyin biyu da kasa tsawatarwa 'yan wasansu a babbar gasar tamaula ta Premier.