Me ya sa har yanzu ba a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ba?

    • Marubuci, Muhannad Tutunji
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Duk da irin zaƙuwar da aka yi don ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas, har yanzu ana samun jan ƙafa kan batun yayin da duka ɓangarorin biyu ke ƙoƙarin daidaita matsalolinsu.

Sanarwar baya-bayan nan da jami'an Isra'ila da Hamas suka fitar, tare da jawaban da masu shiga tsakani suka yi, duka sun nuna alamun cewa ana dab da cimma yarjejeniyar ƙarshe, to sai dai ba a ci gaba da tattaunawar ba.

Rahotonnin gidan radiyon Isra'ila sun nuna cewa sabon sharaɗin da Isra'ila ta gindaya ka iya haifar da tsaiko a yarjejeniyar, kuma ita ma Hamas za ta kawo wata buƙata kan teburin sulhun.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce akwai ci gaba da tattaunawar, amma ya kafe cewa bai san tsawon lokacin da za a ɗauka kafin cimma yarjejeniyar ba.

Ƙasashen Amurka da Masar da Qatar da kuma Turkiyya ne ke jan ragamar tattaunawar domin dakatar da yaƙin da ya shafe tsawon wata 14 ana gwabzawa a Zirin Gaza - wanda aka ƙiyasta cewa an kashe aƙalla mutum 45,000.

Sabbin sharuɗa da sarƙaƙiya

Gidan radiyon Isra'ila ya ce a yanzu ministocin Netanyahu na son Hamas ta rubuto cikakkun sunayen Isra'ilawan da har yanzu take garkuwa da su.

Masu shiga tsakanin sun ce hakan na zuwa ne bayan da tattaunawar ta kai wani mataki mai muhimmanci, yayin da Isra'ila ta ce tana shirye ta zayyano sunayen Falasɗinawan da take tsare da su, waɗanda za ta saki a matsakin farko na yarjejeniyar.

Haka kuma, wasu masu sanya idanu sun ce sharaɗin Isra'ilar na baya-bayan nan ka iya sanya tarnaƙi a yarjejeniyar, kuma har yanzu Hamas ba ta fito da cikakkun sunayen kamar yadda aka buƙata.

Wasu rahotonni na ganin cewa wannan sabon sharaɗin ka iya tsawaita cimma matsayar.

Duk da kalaman Isra'ila na samun ci gaba a tattaunawar, kafofin yaɗa labarai sun ruwaito cewa masu shiga tsakani na Amurka sun fice daga Doha, inda ake tattaunawar. Wannan ya nuna yadda aka samu turjiya a wasu al'amuran.

Wasu majiyoyin Amurka sun ce ɗaya daga cikin batutuwan da suka haifar da turjiya shi ne adadin Isra'ilawan da za a saki a rukunin farko, da kuma bayanan fursunoni Falasɗinawa da za a yi musayar da su.

Baya ga wannan, babban abin da ya ƙara tsawwala yarjejeniyar shi ne har yanzu ba a ɗauki matsaya kan batun wanda zai mulki Gaza bayan cimma matsayar.

Sannan akwai batun buƙatar janyewar Isra'ila daga wasu yankunan, domin bai wa Falasɗinawa da suka rasa muhallansu komawa yankunansu, da kuma batun wanda zai yi iko da mashigar kan iyakoki.

An samu ci gaba amma abubuwa sun yi tsauri

Duk da waɗannan ƙalubale, wasu majiyoyin Isra'ila sun ce akwai alamun cimma matsaya cikin kwanaki.

gidan talbijin na Isra'ila, Channel 12, ya ce ƙasar ta amince da jerin sunayen fursunoni Falasɗinawan da za a saki a matakin farko.

'Wannan na nufin samun nasara,' kamar yadda kafar talbijin ɗin ta bayyana.

Haka kuma, wasu rahotonnin da majiyoyi daga ɓangaren adawa a Isra'ila, sun ce Netanyahun ya gindaya sabon sharaɗin ne da nufin ''kawo jan ƙafa wajen cimma yarjejeniyar''.

Wani abu da ya ƙara dagula yarjejeniyar, shi ne sabbin buƙatun da Hamas ta bijiro da su, wato janyewar dakarun Isra'ila daga Zirin Gaza da kuma yin musayar duka fursunonin a lokaci guda.

Ƙalubalen da Isra'ila ke fuskanta

Jam'iyyun siyasar Isra'ila sun rarrabu dangane da yadda za a amince da yarjejeniyar da kuma kawo ƙarshen kiki-kakar da ake ciki.

Jagoran adawar ƙasar, Yair Lapid ya zargi Netanyahu da fitar da bayanai ga kafofin yaɗa labaran duniya kan rashin amincewarsa na kawo ƙarshen yaƙin - yayin da ake ci gaba da tattaunawar - da nufin wargaza yunƙurin tattaunawar.

Wannan suka, ya nuna yadda aka samu bambance-bambance kan yadda za amagance rikicin, abin da ke nuna irin matsin lambar da Netanyahu ke fuskanta kama daga ɓangaren adawa zuwa iyalan mutanen da ake garkuwa da su a Gaza.

Sannan kuma ga masu nuna adawa da batun a cikin gwamnatinsa - musamman ministan tsaron cikin gida, Itamar Ben-Gvir da ministan kuɗi, Bezalel Smotrich - waɗanda ke nuna adawa da cimma yarjejeniya da Hamas.

Dangane da wannan batu, ministan ma'aiktar da ke kula da 'yan Isra'ila mazauna ƙetare, Amichai Chikli ya fitar da bayanan yarjejeniyar da aka cimma, a matakin farko da ya ƙunshi dakatar da wuta na kwanaki 42.

Wannan dakatar da yaƙi na wucin gadi, zai bayar da dama a samar da cikakken lokacin da za a kammala sauran matakan yarjejeniyar domin tabbatar da aiwatar da duka abubuwan da ɓangarorin biyu suka cimma.

Rawar da Masar da Qatar ke takawa

A ƙoƙarin komawa tattaunawar, wakilan Masar sun isa birnin Doha domin ci gaba da tattaunawar.

Wasu majiyoyin sun tabbatar da cewa yarjejeniyoyin ka iya kai wa matakin ƙarshe, inda ake sa ran bayyana matsayar cikin kwanaki masu zuwa.

Yayin da ake dosar sabuwar shekara, lokaci na ƙara ƙure wa ɓangarorin biyu domin cimma matsayar da za ta kawo ƙarshen yaƙin.

A yayin da duniya ke jiran bayyana matsaya kan cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin, siyasar cikin gida da batutuwan da suka shafi tsaro tsakanin ɓangarorin ka iya zama manyan ƙalubale a tattaunawar.

Abin da ba za a iya hasashe ba

Yossi Kuperwasser, jami'in leƙen asirin Isra'ila kuma masanin harkokin tsari, ya shaida wa BBC cewa yana da matuƙar wahala a iya hasashen abin da yarjejeniyar za ta ƙunsa.

Kuperwasser, wanda a baya ya yi aiki a ma'aikatar tsaron Isra'ila, ya ce: ''babu tabbas kan abin da zai faru a nan gaba. To sai dai akwai damar, amma tana buƙatar amincewar duka ɓangarorin biyu.''

Tsohon Janar ɗin na Isra'ila ya ce duka ɓangarorin biyu na buƙatar cimma yarjejeniyar, yana mai cewa Hamas ta samu rauni bayan raguwar goyon bayan da take samu daga Iran da sauran ƙawayenta a yankin Gabas ta Tsakiya.

To amma, Kuperwasser na ganin cimma yarjejeniyar ba abu ne mai sauƙi ba: ''Yarjejeniyar na da matuƙar tsauri, kuma tana buƙatar amincewar duka ɓangarorin.

Ya bayyana yarjejeniyar a matsayin "abu da da ba za a iya hasashensa ba". Yana mai cewa: "Wata rana, a samu ci gaba, wata rana kuma a samu tarnaƙi.''