Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Amurka: Bayanai kan manufofin waje na Harris da Trump
Zaɓen Amurka: Bayanai kan manufofin waje na Harris da Trump
An wallafa
Yayin da za a gudanar da zaɓen shugabancin Amurka cikin mako mai zuwa, mun yi muku nazarin wasu manyan manufofin 'yan takarar biyu kan ƙasashen waje.
Manyan manufofin ƙasashen wajen dai sun ƙunshi rikicin yankin Gabas ta Tsakiya, da yaƙin Ukraine da kuma alaƙar Amurka da China.
'Yan takarar biyu sun bayyana ra'ayoyi daban-daban kan waɗannan manyan manufofi manufofi.
Yayin da 'yan takarar biyu suka sha bamban a manufofi biyu, ra'ayoynsu sun yi kamanceceniya kan batun alaƙar Amurka da China.