Mene ne makami mai linzami da ke ratsa nahiyoyi?

Rasha ta yi amfani da ƙasar Ukraine a matsayin wani fage ko dandali na yin gwajin makamai - kamar dai yadda shugaban Ukraine ɗin Volodymyr Zelenski.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Mark Shea
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Rasha ta yi amfani da ƙasar Ukraine a matsayin wani fage ko dandali na yin gwajin makamai - kamar dai yadda shugaban Ukraine ɗin Volodymyr Zelenski ya ce.

"Dukkan wasu alamu da suka haɗa da gudu da nisan tafiya sun dace da makami mai linzami mai ratsa nahiyoyi" kamar dai yadda ya faɗa dangane da harin da aka kai birnin Dnipro da ke gabashi da safiyar Alhamis.

Rasha ta ƙi cewa uffan dangane da harin da ƙasashen yammaci da dama suke tababar ko harin na makami mai linzami ne mai ratsa nahiyoyi.

Idan har an tabbatar da cewa harin na makami mai linzamin ne mai ratsa nahiyoyi, to wannan ne zai zama hari irinsa na farko da aka kai da makamin da ake kira ICBM da ba a taɓa amfani da shi ba a duniya.

Yanzu abin tambaya a nan shi ne mene ne makamai masu linzami da ke ratsa nahiyoyi kuma me ya sa amfani da su ya zama wani babban al'amari?

Mene ne makamin ICBM?

Makami mai linzami da ke tafiyar ratsa nahiyoyi ko kuma ICBM na nufin makamai masu linzami da ke ratsa nahiyoyi ko kuma "Intercontinental Ballistic Missile" a Turance, kuma kamar yadda sunan ya bayyana, makamai ne da aka ƙera su domin isar da bama-bamai zuwa wurare masu nisan zango.

Kowane daga cikin makaman na ɗauke da bama-bamai masu dama da za a iya aika su kai tsaye ba tare da an maƙala su a jikin makamin mai linzami ba kuma su je duk wurin da aka nufi su kai hari.

Tarayyar Soviet da aka fi sani da USSR ce ƙasa ta farko da ta fara gwajin makaman na ICBM a watan Agustan 1957.

A yanzu kuma baya ga Rasha, Amurka da kuma China su ma na da irin makaman da dama a rumbunsu na makamai, inda kuma ƙasashe irin su Burtaniya da Faransa da India da Isra'ila da kuma Koriya ta Arewa ke da makaman masu ratsa nahiya yan kaɗan ko kuma nau'in waɗanda ake harbawa ta ruwa.

Makaman ICBM na da dogon zango sannan suna da mugun gudu fiye da makami mai linzami mai gudun ƙiftawar ido.

Yaya nisan tafiyar makamin ICBM take?

Cikakkiyar ma'anar da ake bai wa makami mai linzami mai ratsa nahiyoyi ita ce makamin da ke tafiya mai nisan kilomita fiye da 5,500, inda wasu kuma kan wuce hakan.

Makami mai linzamin da Rasha ta ƙaddamar a ranar Alhamis an haƙƙaƙe cewa an harba shi ne daga yankin Astrakhan da ke kudanci.

Makamai masu linzami masu ratsa nahiyoyi da Rasha ke amfani da su na iya tafiyar kilomita 10,000, kuma abin da hakan ke nufi shi ne makaman da aka harba su daga wannan yanki na Rasha ka iya kai wa har gabashin bakin ruwan Amurka.

Yadda makamin ke gudu

Akwai hasashen cewa Rasha ta yi amfani da makamin mai linzami samfurin RS-26 Rubezh a harin da ta kai Dnipro.

Makamin na da gudun kilomita 24,500 a cikin awa ɗaya wato kimanin kilomita bakwai a kowace daƙiƙa ɗaya.

Ana kiran makaman ne da masu gudun ƙiftawa saboda yadda roka ke ɗauke da su zuwa ƙololowar sararin samaniya kafin sun waiwayo ƙasa da ƙarfi su rikito kan inda aka hara.

Wannan tsarin ne yake ba su damar gudun fanfalaƙi. Sannan hakan na sa su yi wuyar tarewa kamar sauran makamai masu linzami masu shawagi.

Shin ko makamin ICBM na nukiliya ne?

Akwai yiwuwar zuba makamashin nukiliya a cikin makamin na ICBM.

Babu wata shaida da ke nuna cewa makamin mai linzami da Rasha ta harba Dnipro ba ya ɗauke da makamashin na nukiliya.

An dai ce makamin ya je inda ake so amma "ba tare da wani babban tasiri" ba kamar yadda rundunar sojin saman Ukraine ta ce, duk da dai ba su ƙara wani bayani ba dangane da illar da ya yi musamman waɗanda suka mutu ko jikkata.

Yaya tsadar makaman ICBM take?

Ba a san haƙiƙanin kuɗin da Rasha ta kashe ba kan shirinta na samar da makaman masu linzami masu ƙetara nahiyoyi to amma dai mun san adadin abin da Amurka take kashewa.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ƙaddamar da shirinta na samar da makamin mai linzami mai ƙetara nahiyoyi na Sentinel ICBM a watan yuli, inda ta kashe dala biliyan 140.

The Pentagon greenlit its latest Sentinel ICBM programme in July, with a budget of $140bn.

Kuɗin da kowanne daga cikin makaman ya ci ya kai dala miliyan 162 kamar yadda aka rawaito.

Koma dai mene ne kuma ko ta yaya aka ƙera irin waɗannan makamai sun kasance masu tsadar gaske.

Tarayyar Soviet ce ta fara ƙaddamar da hari da makami mai linzami mai ƙetara nahiyoyi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tarayyar Soviet ce ta fara ƙaddamar da hari da makami mai linzami mai ƙetara nahiyoyi.

Me ya sa Rasha ta ƙaddamar da makamin a yanzu?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Idan har ta tabbata cewa makamin da rashar ta harba mai linzami ne da ke ƙetara nahiyoyi to hakan na nufin yaƙin da ake yi a Ukraine na ƙara ƙazanta a daidai lokacin da ya wuce kwanki 1000 ana gwabza shi.

Shigar da dakarun Koriya ta Arewa zuwa yankin Kursk na Rasha,inda dakarun Ukraine suka ƙwace iko da yankin mai yawan murabba'i 1000 a watan Agustan 2024 na nuni da yadda al'amarin ke ƙara ta'azzara.

Ana dai tunanin hakan ne ya sa shugaba Biden ya amince da amfani da makami mai linzami samfurin Atacms kan yankin Rasha a karo na farko sannan kuma an yi amfani da makamai masu linzami da shawagi kirar Burtaniya da Faransa a yankunan Rashar.

Rasha ta sha alwashin mayar da martanin da ya dace idan Ukraine ta zaɓi amfani da makamai masu linzami masu dogon zango wajen kai mata hari.

Wannan ƙaruwar zaman tankiya na zuwa ne a daidai lokacin da zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump ke shirin shan rantsuwa a karo na biyu na yi wa fadar WhiteHouse kome.

Donald Trump ya sha alwashin kawo ƙarshen yaƙin a cikin awa 24, duk da dai ba a fayyace yadda hakan zai yiwu ba.