Ku San Malamanku tare da Malama Aisha Ibrahim Madayana
Ku San Malamanku tare da Malama Aisha Ibrahim Madayana
An wallafa
An haifi Malama Aisha Ibrahim Madayana a garin Gakarko da ke jihar Nassarawa ta Najeriya.
Malamar ta yi karatun firamare da sakandire da jami'a duka a jihar ta Nassarawa.
Malama Aisha na da matakin digiri na biyu a harshen Larabci.
Malamar ta addini ta ce ta fi karkata ɓangaren karatun Alƙur'ani da ilimin fiqihu.
Wani babban ƙalubale da malamar ta ce ta fuskanta shi ne ƙoƙarin karkatar da mata zuwa bin sunnah daga bidi'a.



