Shin Isra'ila za ta iya samun galaba kan Turkiyya idan za su gwabza yaƙi?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

An kafa Isra'ila a ranar 14 ga Mayu, 1948, kuma Turkiyya ta amince da ita cikin ƙasa da shekara guda, a ranar 28 ga Maris, 1949.

Turkiyya ita ce ƙasa ta farko mai rinjayen Musulmi da ta amince da Isra'ila a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta. Amma kusan shekara tamanin bayan haka, al'amura sun sauya sosai.

Yaƙin kwanaki 12 tsakanin Isra'ila da Iran a bara ya yi tasiri sosai wajen nuna ƙarfi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Isra'ila ta zama ƙasar da ta fito daga yaƙin a matsayin wadda ta fi nuna ƙarfin faɗa da ɗaukar matakan soja kamar yadda ake nunawa, yayin da ita kuma Iran ta zama wadda ta fi nuna juriya da iya kai farmaki ƙasashe daban-daban a lokaci guda.

Amurka tana nuna alamun kaucewa shiga dogon rikici da Iran, amma a cikin Isra'ila ana ta maganar cewa Turkiyya za ta iya zama mai haɗari kamar Iran a yankin a nan gaba.

Harin da Isra'ila ta kai kan sansanin sojin saman Abu al-Duhur a Siriya a ranar 18 ga Agusta, da kuma gargaɗin da ƙasashen biyu suka yi wa juna kai tsaye, sun sake tayar da wata muhimmiyar tambaya: Shin Turkiyya da Isra'ila na ƙara kasancewa abokan gaba da juna a Siriya?

Ana kallon takun-sakar Turkiyya da Isra'ila a Siriya a matsayin wadda ta samo asali ne daga sabanin manufofinsu, domin kowace ƙasa na son ganin makomar Siriya ta kasance daban da abin da ɗayar ke nema.

Me ya sa Turkiyya da Isra'ila ke saɓani kan Siriya?

"Turkiyya na son dunƙulalliyar Siriya wadda za ta iya sarrafa iyakokinta, ta haɗa ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai, ta dakile barazanar ISIS da ƙungiyoyin da ke da alaƙa da PKK, sannan ta samar da hanyar dawowar 'yan gudun hijira zuwa ƙasarsu. Tun da Turkiyya tana da iyaka mai kusan kilomita 900 da Siriya, idan Siriya ta sake rushewa ko rarrabuwa, Turkiyya ce za ta fi shan wahala," kamar yadda Buğra Sarı, mataimakin farfesa a fannin hulɗar ƙasa da ƙasa a Jami'ar Mersin, ya rubuta a shafin Middle East Monitor.

Farfesa Buğra ya ƙara da cewa:

"A gefe guda kuma, Isra'ila tana ganin cewa Siriya mai ƙarancin ƙarfi ta fuskar soja ita ce mafita mafi dacewa da tsaronta. Tana son Siriya mai raunin kariyar sararin samaniya, ƙarancin manyan makamai, babu wata ƙasa mai adawa da ita kusa da tsaunukan Golan, kuma ta sami cikakkiyar 'yanci wajen gudanar da ayyukan soja."

A lokacin mulkin Bashar al-Assad, Iran ce ke da babban tasiri a Siriya. Amma bayan Al-Sharaa ya hau mulki, tasirin Turkiyya ya ƙaru. Sakamakon haka, takun-sakar Isra'ila a Siriya ba ta ta'allaka ga Iran kaɗai ba, Turkiyya ma ta zama muhimmin ɓangare a wannan fafatawa ta siyasa da tsaro.

Tsohon Ministan Tsaron Isra'ila, Yoav Gallant, ya shaida wa gidan rediyon 103 FM na Isra'ila a ranar Litinin cewa idan Iran ta raunana, wani zai cike gurbin da ta bari.

Ya kuma bayyana irin wannan ra'ayi a wata maƙala da aka wallafa a watan Fabrairun 2026, inda ya ce Turkiyya ce ƙasar da ta fi yiyuwar cike wannan gibi.

"A Gabas ta Tsakiya, Turkiyya ce ta fi dacewa ta maye gurbin wannan matsayi saboda burinta na faɗaɗa tasiri. Turkiyya ƙasa ce mai ƙarfi da tarihin daular da ta gabata.

Tana tsakanin Asiya da Turai. Bayan Amurka, tana da rundunar soja mafi girma a NATO. Masana'antun tsaronta suna da ƙarfi, jama'arta masu aiki tukuru ne, sannan tattalin arzikinta na daga cikin manyan cibiyoyin masana'antu a Turai. Turkiyya babbar ƙasa ce, kuma tuni ta fara faɗaɗa tasirinta a wurare da dama," in ji Yoav Gallant.

Shin Isra'ila za ta iya samun galaba kan Turkiyya?

Shin Isra'ila za ta iya mu'amala da Turkiyya kamar yadda ta yi da Iran? Shin tana da ƙarfin shiga yaƙi da Turkiyya ta fuskar soja?

Farfesa Ashwini Mahapatra na Cibiyar Nazarin Yammacin Asiya ta Jami'ar Jawaharlal Nehru da ke New Delhi ya yi tsokaci.

"Idan aka kwatanta da Iran, yaƙi tsakanin Isra'ila da Turkiyya al'amari ne daban gaba ɗaya. Dukan su ƙasashe ne masu muhimmiyar rawa a yankin. Lokacin da Isra'ila ta yi yaƙi da Iran, ta samu goyon bayan Amurka. Amma Turkiyya mamba ce ta NATO. Idan aka kai hari ga mambar NATO, ana iya kallon hakan a matsayin hari ga dukkan ƙawayen NATO. Wannan shi ne babban ƙalubalen."

Dangane kuma da ƙarfin sojin ƙasashen biyu, Farfesa Ashwini Mahapatra ya ƙara da cewa:

"Idan aka dubi rundunonin sojin Isra'ila da Turkiyya, Turkiyya ta rage dogaro da ƙasashen waje sosai wajen samar da ƙarfin sojinta a cikin shekaru goma da suka gabata.

Tana samar da jiragen yaƙi marasa matuƙa da kanta kuma tana fitar da su zuwa wasu ƙasashe. Yanzu ma ta fara ƙera jiragen yaƙi. Sabunta rundunar sojinta ya fara ne tsakanin 1978 zuwa 1980 lokacin da Amurka ta ƙaƙaba mata takunkumin makamai. Tun daga lokacin take ƙoƙarin rage dogaro da wasu ƙasashe. A cikin shekaru 30 zuwa 40 da suka gabata, ta samu ci gaba sosai."

Ƙarfin jurewa yaƙi

Bugu da ƙari, Farfesa Mahapatra ya ƙara da yin bayani dangane da arziƙin da kowacce ƙasar ke da shi domin jurewa yaƙin.

"Ina ganin Isra'ila ba ta da isassun albarkatu da za ta iya yaƙar Turkiyya. Ta fuskar ƙarfin sama, Isra'ila na da wani ƙaramin rinjaye, amma idan Turkiyya ta samu jiragen F-35 na Amurka, wannan rinjaye zai gushe. Rundunar ruwan Turkiyya ma tana da ƙarfi sosai. Saboda haka, a halin yanzu Turkiyya ta fi Isra'ila ƙarfi."

Har yanzu Turkiyya ba ta cikin ƙasashen da Turai da Amurka ke kallon su a matsayin babbar barazana ga duniya kamar yadda suke kallon wasu ƙasashe. Don haka, matsayin Amurka game da Turkiyya ba zai iya zama daidai da yadda take mu'amala da Iran ba.

Kuma ko da Amurka ta so ɗaukar irin wannan matsayi, hakan ba zai kasance mai sauƙi ba.

Jakadan Amurka a Turkiyya, Tom Barrack, ya kuma yi Allah-wadai da harin da Isra'ila ta kai kan wani filin jirgin saman soji a Siriya kusa da iyakar Turkiyya.

Ya ce an kai harin ne duk da tabbacin da Amurka ta bayar da kuma tabbatarwar Turkiyya cewa ba za ta girke sojojinta a wurin ba.