Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Nawa ne kuɗin da mutum zai kashe idan zai yi takarar shugaban ƙasa a Najeriya?
Yayin da ƴan siyasar Najeriya suka sake fara yaƙin neman zaɓe gabanin babban zaɓen 2027, ana ci gaba da tambaya kan yawan kuɗin da ake buƙata domin gudanar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa.
Kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe sun haɗa da tallace-tallace, shirya gangami, sufuri da sauran kayan aiki, tara magoya baya, da kuma gudanar da ayyuka a ranar zaɓe.
Tuni jam'iyyar APC mai mulki ta sanar da kwamitin yaƙin neman zaɓenta, inda ta naɗa Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, a matsayin daraktan tara kuɗaɗen yaƙin neman zaɓen.
Ana kuma sa ran manyan jam'iyyun adawa biyu, ADC da NDC, za su sanar da nasu kwamitocin yaƙin neman zaɓe nan ba da jimawa ba.
Masana da masu bibiyar harkokin siyasar Najeriya sun ce yana da wahala a iya tantance ainihin adadin kuɗin da ake kashewa.
A wannan labarin, za mu duba hanyoyin da 'yan takara da jam'iyyun siyasa ke samun kuɗin yaƙin neman zaɓe, abin da doka ta tanada kan iyakar kashe kuɗi, ƙiyasin kuɗin da aka kashe a yaƙin neman zaɓen baya, da kuma yadda hukumomi ke sa ido kan yadda ake kashe kuɗin siyasa.
Nawa ake tarawa domin yaƙin neman zaɓe?
A tsawon shekaru, jam'iyyun siyasa sun ɓullo da hanyoyi daban-daban na tara kuɗaɗen da za su gudanar da yaƙin neman zaɓensu. Wasu daga cikin waɗannan hanyoyin sun haɗa da:
- Sayar da fom ɗin tsayawa takara
- Gudummawa daga mutane da ƴan kasuwa
- Tara kuɗi daga jama'a, wato crowdfunding
Alal misali, gabanin zaɓen 2027, APC ta samu biliyoyin naira daga sayar da fom ɗin tsayawa takara ga ƴan jam'iyyar a mukamai daban-daban.
Mafi tsada shi ne fom ɗin takarar shugaban ƙasa, wanda ya kai naira miliyan 100, kuma mutane biyu ne suka saya - Shugaba Tinubu da wani Stanley Osifo. Mafi arha kuma shi ne fom ɗin takarar Majalisar Dokokin Jiha, wanda ya kai naira miliyan shida.
Shugabannin APC sun shaida wa manema labarai cewa kusan mutum 2,980 ne suka sayi fom domin tsayawa takara a muƙamai daban-daban. Idan aka ɗauka cewa dukkansu sun sayi fom mafi arha na naira miliyan shida, APC za ta samu sama da naira biliyan 17.
Haka lamarin yake ga sauran manyan jam'iyyun siyasar ƙasar, kamar ADC wadda fom ɗin takarar shugaban ƙasarta ya kai naira miliyan 90, yayin da NDC ta sayar da nata kan naira miliyan 60.
Haka kuma, jam'iyyun siyasa kan gayyaci manyan ƴan kasuwa da kamfanoni a ƙasar domin ba da gudummawar kuɗi don tallafa wa yaƙin neman zaɓensu, kuma a mafi yawan lokuta, gudummawar da masu bayar da ita - ko kuma ɗaya daga cikinsu - ba cika bayyana su ba.
Sai dai akwai masu bayar da gudummawa da ke bayyana abin da suka bayar a bainar jama'a, kamar yadda ya faru a 2018 lokacin da attajirin ɗan kasuwar man fetur, Arthur Eze na jihar Anambra, ya bayyana cewa ya bayar da gudummawar naira biliyan ɗaya domin tallafa wa yaƙin neman zaɓen sake zaɓen tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, wanda yanzu shi ne ministan ayyuka na Najeriya.
Haka kuma akwai tsarin tara kuɗi daga jama'a, wato crowdfunding, salon da jam'iyyun siyasa da ƴan takararsu ke amfani da shi wajen neman gudummawa daga talakawa waɗanda ba su da kuɗi masu yawa.
A shekarar 2022, APC ta ƙaddamar da wata manhajar wayar hannu mai suna 'Bless Me', inda ta nemi ƴan Najeriya su sauke manhajar kuma su yi amfani da ita wajen bayar da gudummawar kuɗi cikin sauƙi ga yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Tinubu.
Daga baya ta sanar da cewa mintuna kaɗan bayan ƙaddamar da manhajar, ta samu gudummawar sama da naira miliyan 190 daga mutane a sassa daban-daban na Najeriya.
Haka kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi amfani da wannan hanyar ta tara kuɗi daga jama'a.
Aisha Yesufu, ƴar fafutukar kare haƙƙin bil'adama kuma mai goyon bayan Peter Obi, ta sanar da cewa sun tara kusan naira miliyan 595 ta wannan hanyar.
Nawa doka ta amince ƴan takara su kashe?
Dokar zaɓen Najeriya ta bayyana adadin kuɗin da ƴan takara da jam'iyyun siyasarsu za su kashe a lokacin yaƙin neman zaɓe, sai dai tabbatar da tsarin na aiki wannan wani batu ne daban.
Sashe na 92 na Dokar Zaɓe, ƙarƙashin ƙaramin sashe na 1 zuwa 7, ya ƙayyade kuɗin da za a iya kashewa zaɓe kamar haka:
Dokar ta ce: "Ɗan takarar shugaban ƙasa ba zai kashe kuɗin da ya wuce naira biliyan 10 ba."
- Zaɓen Gwamna - naira biliyan 3
- Zaɓen Sanata - naira miliyan 500
- Zaɓen Majalisar Wakilai - naira miliyan 250
- Zaɓen Majalisar Dokokin Jiha - naira miliyan 100
- Zaɓen Shugaban ƙaramar hukuma/Kansila - naira miliyan 100
- Zaɓen Kansila - naira miliyan 10
Dokar Zaɓen ta kuma ce "ba a yarda wani mutum ko wata ƙungiya su ba ɗan takara gudummawar da ta wuce naira miliyan 500 ba."
Kafin wannan sauyin, adadin kuɗin bai kai haka baa.
Misali, a zaɓen 2023, ɗan takarar shugaban ƙasa ba zai iya kashe fiye da naira biliyan 5 ba, amma yanzu an ƙara adadin zuwa naira biliyan 10.
Haka kuma, a shekarar 2023, gudummawar da mutum zai iya bai wa ɗan takarar shugaban ƙasa ita ce naira miliyan 50, amma yanzu ya ninka sau goma zuwa naira miliyan 500.
Abin da ƴan takara suka kashe a zaɓen da ya gabata
Babu wata hanya bayyananniya da ake amfani da ita wajen sa ido kan adadin kuɗin da jam'iyyun siyasa da ƴan takararsu ke kashewa a lokacin zaɓe.
Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ba ta bibiyar irin waɗannan bayanai, saboda ba sa cikin ayyukan da aka ɗora mata. Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ce ke da hurumin doka na sanya ido kan yadda ake kashe kuɗin yaƙin neman zaɓe da kuma tabbatar da cewa jam'iyyun siyasa ba su karya dokar ba.
Sai dai bayan zaɓen 2023, wasu jam'iyyun siyasa sun wallafa bayanan kuɗin da suka kashe a yaƙin neman zaɓensu da kansu.
Ɗaya daga cikinsu ita ce Labour Party, inda mai kula da tara kuɗaɗen yaƙin neman zaɓen jam'iyyar, Aisha Yesufu, ta ce sun kashe kusan naira biliyan 1.395 a zaɓen, ciki har da sama da naira miliyan 744 da aka kashe wajen shari'o'in da suka biyo bayan zaɓen.
Kwamitin yaƙin neman zaɓen Peter Obi ya ce hanyoyin da suka samu kuɗin sun haɗa da kusan naira miliyan 596 da aka samu a matsayin gudummawa daga ƴan Najeriya da ke cikin gida da ƙasashen waje, da kuma naira miliyan 800 da Peter Obi da kansa ya bayar.
Wata jam'iyyar da ta wallafa rahoton kuɗaɗen yaƙin neman zaɓenta na 2023 a bainar jama'a ita ce African Action Congress (AAC), wadda ɗan takararta na shugaban ƙasa shi ne ɗan fafutukar kare haƙƙin bil'adama, Omoyele Sowore.
Rahoton jam'iyyar ya nuna cewa ta kashe kusan naira miliyan 40 ne kacal a yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Ta wace hanya INEC ke sanya ido kan kashe kuɗaɗen?
A cewar Dokar Zaɓe, INEC da jam'iyyun siyasa ne ya kamata su haɗa kai wajen tantance adadin kuɗin da kowace jam'iyya ta kashe wajen yaƙin neman zaɓe, da kuma tabbatar da cewa ba su wuce adadin da doka ta tanada ba.
Sashe na 93(3) na Dokar Zaɓe ya ce jam'iyyun siyasa suna da watanni shida bayan kowane zaɓe su gabatar wa INEC da rahoton kuɗaɗen da suka kashe wajen yaƙin neman zaɓe.
Dole ne mai binciken kuɗaɗen jam'iyyar da shugabanta na ƙasa su sanya hannu kan rahoton, tare da rantsuwar da za su yi a gaban kotu cewa rahoton da aka gabatar sahihi ne.
Hukuncin da jam'iyyar da ta gaza gabatar da rahoton cikin wa'adin da aka kayyade za ta fuskanta shi ne tarar naira miliyan 10, ko kuma kotu ta ci tarar ta naira miliyan ɗaya a kowace rana har sai ta gabatar da rahoton.
Dokar ba ta bayyana ko INEC za ta wallafa waɗannan rahotanni a bainar jama'a domin ƴan Najeriya su san abin da ke cikinsu ba.
Sai dai masana da ƙungiyoyin fararen hula sun ce wannan tanadi ba shi da wani tasiri, kuma INEC ma ba ta aiwatar da shi yadda ya kamata.
Ƙungiyar SERAP ta yi kira ga INEC da ta sanya ido tare da tsara yadda ake bayar da tallafin kuɗi da kuma gudanar da harkokin kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe na 'yan takara da jam'iyyunsu gabanin zaɓen 2027.
Ɗaya daga cikin manyan jami'an SERAP, Kolawole Oluwadare, ya kuma buƙaci INEC ta wallafa rahotannin da aka tantance na kuɗaɗen da jam'iyyun siyasa suka kashe wajen yaƙin neman zaɓe daga 2023 zuwa 2025.
"Ƙara bayyana yadda ake tafiyar da kuɗaɗen siyasa na da muhimmanci wajen tabbatar da cewa zaɓen 2027 ya gudana cikin daidaito, ta yadda 'yan ƙasa za su iya yin zaɓin siyasa cikin 'yanci da kuma bisa cikakken bayani," in ji Oluwadare ya a cikin wata sanarwa da SERAP ta fitar ranar 23 ga Agustan 2026.