Ra'ayi Riga: Yadda dakatar da tallafin USAID zai shafi Najeriya 21/02/2025

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Ra'ayi Riga: Yadda dakatar da tallafin USAID zai shafi Najeriya 21/02/2025
An wallafa

Ɗaya daga cikin abubuwan da suka ɗauki hankalin ƴan Najeriya a baya-bayan nan shi ne batun cewa USAID na da hannu a ta'addancin da ke faruwa a Najeriya.

A ranar 13 ga watan Fabrairu ne wani ɗan majalisar Amurka, Scott Perry ya zargi USAID da tallafa wa ƙungiyoyin ta'addanci a ƙasashen duniya, ciki har da Boko Haram.

Perry ya ce tallafin USAID kai tsaye ya amfani ƙungiyoyin ta'adda a duniya kamar Boko Haram da Al-Qaeda da ISIS.

Sai dai Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills ya musanta batun a wata ganawa da ƙungiyar gwamnonin Najeriya a Abuja da daren Laraba, inda ya ce babu wata hujjar da ke nuna hakan.

Maganar ta matuƙar tayar da ƙura a Najeriya, musamman kasancewar dama wasu da dama sun kasance suna zargin akwai hannun ƙasashen waje a harkokin ta'addanci a ƙasar.

Shin yaya lamarin yake ne?

Yaya masana suke kallon wannan zargin?

Mene ne tasirin wannan zargin kan yaƙi da ta'addanci?

Waɗannan na daga cikin batutuwan da muka tattauna a cikin shirin namu na Ra'ayi Riga na wannan makon.