Man City ta ci gaba da zama ta biyar a teburin Premier

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta tashi 2-2 da Brighton a wasan mako na 29 a Premier League ranar Asabar a Etihad.
Erling Haaland ne ya fara cin ƙwallo a bugun fenariti tun a minti na 11 da take leda, daga baya Brighton ta farke ta hannun Estupina a minti na 21.
Tun kan hutu City ta kara na biyu a raga ta hannun Omar Marmoush, bayan da aka koma zagaye na biyu Brighton ta farke, sakamakon da Khusanov ya ci gida.
Ƙwallon da Haaland ya ci ya zama na farko da yake da hannu a cin 100 a karancin wasa, wanda ya ci 84 ya bayar da 16 aka zura a raga a karawa ta 94.
Da wannan sakamakon City ta ci gaba da zama ta biyar a teburin Premier da maki 48 da tazarar maki ɗaya tsakani da chelsea ta huɗu da za ta kara da Arsenal ranar Lahadi.
Ita kuwa Brighton mai maki 47 tana ta bakwai, sakamako nasara 12 da canjaras 11 aka doke ta shida daga wasan mako na 29.
Manchester City za ta fafata a gidan Bournemouth a FA Cup ranar Lahadi 30 ga watan Maris daga nan ta kara da Leicester a Premier ranar 2 ga watan Afirilu a Etihad.
Brighton kuwa za ta karɓi bakuncin Nottingham Forest ranar Asabar 29 ga watan Maris a FA Cup daga nan ta kece raini da Aston Villa a gida a Premier ranar 2 ga watan Afirilu.










