Abin da ya sa Isra'ila ke kai hare-hare cikin Syria bayan hamɓarar da Assad
Abin da ya sa Isra'ila ke kai hare-hare cikin Syria bayan hamɓarar da Assad
An wallafa
Bayan hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad da aka yi a Syria, Isra'ila tana kai hare-hare zuwa ƙasar ta sama.
Ita dai Isra'ila tana iƙirarin cewa tana kai hare-haren ne domin hana makamai masu guba da marasa guba faɗawa hannun 'yantawaye masu tsattauran ra'ayi.
Isra'ilar ta ce ta kai hari kan sansanonin jiragen ruwa da filayen jirgin sama da rumbanan ajiyar makamai da cibiyoyin bincike.
To sai dai ƙasashen Larabawa da dama da wasu na Turai sun sok matakin, inda suek zargin cewa Isra'ila na hakan ne domin faɗaɗa iko a wuraren da ke ƙarƙashinta a yankin.



