Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Letexier zai yi raflin wasan Real da Arsenal a Champions League
Francois Letexier ne zai yi alkalancin wasan Real Madrid da Arsenal da za su kara a Santiago Bernabeu ranar Laraba in ji Uefa.
Real Madrid za ta karɓi bakuncin Gunners a wasa na biyu a gasar zakarun Turai zagayen kwata fainal.
A makon jiya, Arsenal ta doke Real Madrid 3-0 a Emirates a gasar ta zakarun Turai.
Wannan shi ne karo na biyar da raflin ɗan kasar Faransa zai busa wasan da ya shafi Real Madrid a gasar zakarun Turai.
Waɗanda za su taimaka masa aiki sun haɗa da Cyril Mugnier da kuma Mehdi Rahmouni, dukkansu daga Faransa.
Jérôme Brisard ne zai kula da VAR da kuma Bastien Dechepy mataimakinsa, sai Stéphanie Frappart a matakin mai jiran ko-ta-kwana.
Wasannin da Letexier ya busa a Champions League da Real Madrid:
- Liverpool 2-0 Real Madrid (wasa na biyar a rukuni a 2024/25)
- Real Madrid 3-3 Manchester City (kwata fainal zagayen farko a 2023/24)
- Real Madrid 4-2 Nápoles (wasa na biyar a cikin rukuni a 2023/24)
- Real Madrid 2-0 Chelsea (kwata fainal zagayen farko 2022/23)