Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Champions League: Abubuwan da ba ku sani ba kan wasan Inter da PSG
A yau Asabar, 31 ga watan Mayu ne za a fafata wasan ƙarshe na gasar Champions League, wanda za a buga a filin wasan Munich Football Arena da ke Munich a ƙasar Jamus.
Za a ɓarje gumi tsakanin ƙungiyar PSG ta Faransa da Inter Milan ta Italiya, wanda kusan shi ne wasa babba da ake tsimayi a kakar wasan ƙwallon ƙafa ta bana wadda ake ƙarƙarewa.
Real Madrid ce ta lashe gasar ta kakar bara, inda ta doke ƙungiyar Dortmund ta Jamus da ci biyu da nema a wasan ƙarshe a filin wasa Wembley da ke birnin London na Ingila.
Ana hasashen wasan zai yi zafi ne kasancewar PSG na fafutikar samun nasara babba domin kwantar da hankalin shugaban ƙungiyar, Nasser Al-Khelaifi, wanda tun zuwansa ƙungiyar yake zuba kuɗaɗe maƙudai wajen ɗauko manyan ƴanƙwallon duniya, amma ƙungiyar ga gaza lashe kofin na zakarun turai wanda ake gani ya fi daraja a turai.
A ɗaya ɓangaren, ita kuma Inter Milan duk da ta taɓa lashe gasar a baya, tana ganin wannan wata dama ce da za ta sake lashe gasar karo uku a shekarun 1964 da 1965 da 2010.
Kafin wannan wasan na yau, an buga wasa 188, inda aka zura ƙwallo 613 da sauran abubuwa da suka faru a gasar mai ɗaukar hankali.
Muhimman abubuwa kan wasan
Wannan ne karo na farko da ƙungiyoyin biyu za su fafata a wasan zakarun turai, kuma na biyu da za a fafata wasan ƙarshe a gasar tsakanin kulob daga Faransa da ta Italiya.
A na farkon, an buga wasa ne tsakanin Marseille da Milan a kakar 1992/1993, wanda Marseille ta doke Milan da ci ɗaya mai ban haushi, kuma shi ma wasan a birnin Munich aka buga a filin wasa na Olympiastadion.
A shekarar 2020 ce PSG ta samu damar lashe kofin, amma Bayern Munich ta doke ta a birnin Lisbon, wanda hakan ya sa Inter Milan ta zarce ta, kasancewa ta lashe kofin uku.
Ita dai PSG ta fara ne da rarrafe da tata-burza a farkon gasar ta bana, wadda aka yi da sabon tsari. Amma daga baya sai ta murmure bayan ta ƙara ƙaimi, inda ta lashe wasanni uku na ƙarshe, ta zo ta 15 a teburi, wanda ya ba da damar tsallakawa zagaye na biyu.
Bayan ta samu tsallakewa zuwa zagaye na gaba, sai ta fara nuna rawar gani, inda ta doke Liverpool a bugun fanareti, sannan ta doke Aston Villa da Arsenal.
Ita kuma Inter Milan tun farko dama da ƙarfinta ta fara, inda ta zo ta huɗu a zagaye na farko na gasar.
Wasa ɗaya kawai ta yi rashin nasara, wanda Bayer Leverkusen ta doke ta da ci ɗaya da nema, kuma kuma shi ne ƙwallon farko da aka tura mata a raga.
A zagaye na biyu kuma ƙungiyar ta doke Feyenoord da Bayern Munich da Barcelona kafin ta kai wasan ƙarshe.
PSG ce ƙungiya daga Faransa ta uku da ta kai wasan ƙarshe a gasannin turai: European Cup da Champions League sama da sau ɗaya bayan ƙungiyar Reims wadda ta samu damar zuwa wasan ƙarshe a kakar 1955/56 da kuma kakar 1958/59, sai Marseille a kakar 1990/91 da kakar 1992/93.
Ƙungiyar ta samu nasara a wasa 9 daga cikin wasa 11 da ta buga a gasar ta bana, sannan ta yi kunnen-doki biyu, sannan ita ce take fara zura ƙwallo a wasa bakwai cikin tara da ta samu nasara.
Inter kuma ta samu nasara a wasa 10 a gasar a kakar bana - wanda ita ce wadda ta fi samun nasara a gasar. Wasa ɗaya kawai ta yi rashin nasara a wasa 14 da ta buga a gasar a bana, sannan wasa takwas ke nan ba ta rasa ba. Ta ci shida, ta yi kunnen-doki biyu.
Dukansu sun taɓa rashin nasara a wasan ƙarshe na zakarun turai. Bayern Munich ta doke PSG a 2020, ita kuma Man City ta doke Inter a shekarar 2023.
Ƴanwasa
PSG: Donnarumma; Hakimi, Marquinhos, Pacho, Nuno Mendes; João Neves, Vitinha, Fabián Ruiz; Kvaratskhelia, Dembélé, Barcol
Inter Milan: Sommer; Pavard, Acerbi, Bastoni; Dumfries, Barella, Çalhanoglu, Mkhitaryan, Dimarco; Lautaro Martínez, Thuram