Nathan Ake zai kara yin jinya bayan tiyata da aka yi masa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan Manchester City, Nathan Ake zai kara yin jinya, bayan da aka yi masa tiyata, sakamakon karya kafa da ya yi.

Ɗan wasan tawagar Netherlands, mai shekara 30, an sauya shi a FA Cup da City ta fitar da Plymouth ranar Asabar, ana cewa zai yi jinya mai tsawo.

Ake ya saka hotonsa a kafar sada zumunta, bayan da aka kammala yi masa tiyatar.

Wasa 18 Ake ya buga a kakar nan, bayan da ya sha fama da jinya.

Mai tsaron baya, John Stones da kuma Manuel Akanji ba su buga FA Cup ba ranar Asabar, saboda jinya da suke yi.

City mai rike da Premier League tana ta huɗun teburi da maki 47, bayan cin wasa 14 da canjaras biyar aka doke ta karo takwas.

Ranar Asabar City za ta je gidan Nottingham Forest, domin buga wasan mako na 28 a Premier League.

Daga nan City za ta karɓi bakuncin Brighton a babbar gasar tamaula ta Ingila a Etihad ranar Asabar 15 ga watan Maris.