Lafiya Zinariya: Yadda zamantakewa ke janyo matsananciyar damuwa ga mata

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Lafiya Zinariya: Yadda zamantakewa ke janyo matsananciyar damuwa ga mata
An wallafa

Matsananciyar damuwa cuta ce da ta shafi kwakwalwar ɗan Adam, kuma cuta ce da ake samunta a fadin duniya, a cewar hukumar lafiya ta duniya.

Inda ta ƙara da cewa mata sun fi maza fuskantar wannan matsalar a duniya.

Mutanen da suka fuskanci wani mummunan tashin hankali, cin zarafi, ko wani mummunan iftila'i na rayuwa sun fi shiga hatsarin kamuwa da matsananciyar damuwa. In ji hukumar.

Sai dai akwai hanyoyin rage kaifin cutar ko magance ta da suka hada da ba da baki da magunguna.

Ko da yake hukumar ta yi ƙiyasin cewa fiye da kashi 75 cikin ɗari, na masu fama da matsananciyar damuwa a kasashen da ke da ƙaranci da matsakaicin kuɗin shiga, basa samun kulawar ma'aikatan lafiya.

Cibiyar kula da matsalar kwakwalwa ta Amurka ta bayyana wasu daga cikin alamomin cutar kamar haka:

  • Yawan fargaba da saurin fushi
  • Yanke ƙauna
  • Daina jin daɗin abubuwan da suke faranta rai
  • Yawan gajiya, rashin karsashi da jin cewa babu abin da ke da daɗi
  • Kasa mayar da hankali a kan abu, kasa tuna abin da ya faru da gaza yanke hukunci
  • Sauyi a yanayin barci ko na cin abinci
  • Yawan jin ciwon jiki musamman wanda babu wata alama ta zahiri
  • Tunanin kashe kai ko yunkurin hakan