Wane ne Jeffrey Epstein: hamshaƙin ‘kawalin’ shugabanni da attajiran duniya?

Jeffery Epstein sanye da baƙar riga da gilashi

Asalin hoton, US Department of Justice

Bayanan hoto, Wani bidiyo ya nuna Epstein ana hira da shi, inda ake tambayar ko shi 'sheɗani' ne
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

"Ni ba mai cin zarafin ƴan mata ba ne," in ji Jeffrey Epstein a zantawarsa da jaridar New York Post a 2011. "Akwai bambanci tsakani mai kashe mutane da ɓarawon burodi."

Epstein ya rasu ne a gidan yarin New York a ranar 10 ga Agustan 2019 a daidai lokacin da yake zaman dakon shari'arsa kan zarginsa da safarar ƴan mata da cin zarafinsu.

Ya rasu ne kimanin shekara 10 bayan an yanke masa hukunci bisa samunsa da laifin saka ƙananan yara a karuwanci.

Amma a shari'ar ta baya, an zarge shi ne da jagorantar wani gungun ƴan mata ƙanana da yake haɗa su da maza, zargin da ya musanta.

A watan Nuwamban 2025 ne majalisun Amurka suka amince da a fitar da sakamakon binciken kundin Epstein, inda daga bisani Donald Trump ya sanya hannu a takardar buƙatar ɓangaren shari'ar ƙasar ta fitar da kundin.

A ranar 30 ga Janairu ne aka fitar da takardu sama da miliyan da aka tattara bayanan harƙallar Epstein.

Mataimakin Atoni Janar na Amurka Todd Blanche ya ce fitar da kundin ya kawo ƙarshen bincike da kai-komo da ake yi kan buƙatar kundin.

Sai dai har yanzu wasu, musamman ƴan jam'iyyar hamayya ta Democrats na zargin cewa ɓangaren shari'ar ƙasar ya rage tare da ɓoye wasu bayanan ba tare da cikakken bayani ba.

Abota da Trump

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A New York aka haifa Epstein, kuma a birnin ya girma, sannan ya koyar da darasin lissafi da physics a makarantar Dalton mai zaman kanta a tsakankanin shekarun 1970s.

A jami'a ma ya karanta nazarin physics da lissafi ne, amma bai kammala karatun jami'a ba.

Wani mahaifin ɗalibinsa ya saka shi a cikin harkokin kasuwancinsa, inda ya ba shi babban matsayi a Wall Street investment bank Bear Stearns, ya yi aiki na shekara huɗu, kafin ya buɗe nasa mai suna J Epstein and Co.

Kamfanin ne ya riƙa kula da kadarorin abokan hulɗarsa na kusan dala biliyan 1, kimanin fam miliya 800, ida ya zama hamshaƙin attajiri.

A lokacin ne Epstein ya fara rayuwa ta alfarma, ciki har da mallakar gidan alfarma a Florida da gidan gona a New Mexico sannan ya fara mu'amala da fitattun mutane da ƴan siyasa.

"Na san Jeff sama da shekara 15 da suka gabata," in ji Shugaban Amurka Donald Trump a zantawarsa da mujallar New York a game da kundin Epstein a 2002.

Shugaban ya ce sun ɓata ne a 2000, shekara ɗaya kafin a kama Epstein, sannan ya nanata cewa bai ga wani laifin da ya aikata ba kawai domin ya yi mu'amala da Epstein.

Fadar gwamnatin Amurka ta ce Trump ya taɓa fatattakar Epstein daga gidan shaƙatawarsa, sannan Trump da kansa ya bayyana cewa Epstein yana "sace" ƴan mata ƙanana da suke masa aiki a wajen shaƙatawa na Mar-a-Lago beach club spa.

Jeffrey Epstein da Donald Trump a Florida a 1997

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jeffrey Epstein da Donald Trump a Florida a 1997

A 2002 ya yi tafiya tare da tsohon shugaban Amurka, Bill Clinton da jaruman fim Kevin Spacey da Chris Tucker a jirgin yawo.

Ya yi yunƙurin mallakar mujallar New York a 2003, amma aka ƙi sayar masa, sannan a shekarar ya bayar da gudunmuwar dala miliyan 30, kimanin fam miliyan 23 ga Jami'ar Harvard.

Tuni dai Bill Clinton da matarsa Hillary Clinton suka amince su bayyana a gaban majalisar Amurka domin bayar da bayani kan bincike da ake ci gaba da yi kan kundin na Epstein.

Haka kuma Epstein ya kasance abokin fitaccen ɗan siyasar Birtaniya Peter Mandelson – duk da cewa Mandelson ya ce ya yi da-na-sanin abotar, saboda abotar ce ta sa aka cire shi a matsayin ambasan ƙasar a Amurka a 2025.

Sai dai duk da abota da yake yi da manyan mutane a duniya, Epstein ya zaɓi gudanar da rayuwarsa a ɓoye, inda ba a cika ganinsa a tarukan mutane ba, ko wajen cin abinci da sauran wuraren shaƙatawa.

Ya yi soyayya da ƴan mata irin su tsohuwar sarauniyar kyawun Sweden Eva Andersson Dubin da Ghislaine Maxwell, wadda ƴa ce ga mawallafi Robert Maxwell, amma bai taɓa aure ba.

Fuskantar shari'a

A 2005 ne iyayen wata yarinya mai shekara 14 ta kai ƙara wajen ƴansanda a Florida cewa Epstein ya ci zarafinta a Palm Beach.

"Ba ya ɓoye sha'awar da yake yi wa ƙananan ƴan mata," in ji marubuci Michael Wolff a shekarar 2007.

"Akwai lokacin da muke magana da shi bayan an fara maganar kundin, inda ya bayyana min cewa lallai yana son ƙananan ƴan mata."

Sai dai ya samu nasarar ƙulla yarjejeniyar da wani mai gabatar da ƙara a shekarar 2008.

Hakan ya sa ya samu sauƙin hukunci, inda aka yanke masa hukuncin wata 18 a gidan yari maimakon hukuncin ɗaurin rai da rai.

An soki Andrew Mountbatten-Windsor, ko kuma Yarima Andrew bisa alaƙarsa da Jeffrey Epstein

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An soki Andrew Mountbatten-Windsor, ko kuma Yarima Andrew bisa alaƙarsa da Jeffrey Epstein

Jaridar Miami Herald ta ruwaito cewa mai gabatar da ƙara na tarayya Alexander Acosta ne ya yi cuwa-cuwar rage zafin laifuka Epstein domin rage masa hukunci.

Acosta ya ajiye aiki a watan Yulin 2019 saboda samunsa da laifin harƙallar ɓoye bayanai game da binciken, duk da cewa ya kare matakin da ya ɗauka.

Tun daga shekarar 2008 Epstein yake cikin waɗanda aka ayyana a matsayin masu laifin cin zarafin mata, inda yake mataki na uku, wanda ke nufin an sa ido a kansa, domin zai iya komawa ruwa ko da ya ce ya daina.

Amma dai Epstein ya ci gaba da mallakar kadarorinsa har bayan da ake yanke masa hukunci.

A watan Disamban 2010 ne aka ga hoton Andrew Mountbatten Windsor - ɗan Sarauniya Elizabeth, wanda a lokacin yake riƙe da sarautar Yarima Andrew tare da Epstein a danalin New York.

A zantawarsa da BBC a watan Nuwamban 2019, Andrewa ya ce ya san Epstein ne tun a 1999, amma a 2010 ya je har New York domin su kwance abotar, sannan ya ce ya yi da-na-sanin abotar.

Wata wadda take zargin Epstein da cin zarafinta mai suna Virginia Roberts wadda ta koma amsa sunan Virginia Giuffre ta yi zargin cewa an haɗa ta da Andrew ya yi lalata da ita tun tana ƴar shekara 17.

Sai dai Andrew ya musanta zargin cewa ya yi lalata da ita, amma a shekarar 2022 ya biya miliyoyin daloli ga Ms Giuffre domin samun maslaha bayan ta shigar da ƙara a kotu cewa ya yi lalata da ita tana ƙarama.

Yanzu an samu wani sabon bayani da ke nuna alaƙar Epstein da tsohuwar matar Andrew, Sarah Fergusson.

Masu gabatar da ƙara dai sun bayyana buƙatar a ƙwace kadarorin Epstein, ciki har da babba gidansa da alfarma a New York, inda ake tunanin yawancin baɗalar da ake zarginsa da aikatawa a ciki aka yi, duk da cewa ya sha nanata cewa shi bai aikata laifin komai ba.

Shari'ar Maxwell

Bayan mutuwar Epstein, sai aka fara maganar tsohuwar budurwarsa Ghislaine Maxwell.

An kamata ne a watan Yulin 2020 bisa zarginta da taimakonsa wajen aikata laifukan cin zarafi.

A watan Disamban 2021, wani alƙali a New York ya same ta da laifuka biyar daga cikin shida da ake tuhume ta su, inda aka yanke mata hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari a lokacin tana da shekara 60 a duniya.

Ana tunanin Maxwell ce ta haɗa Epstein da wasu abokan hulɗarta irin su Bill Clinton da Andrew.

Ana tunanin duk da cewa alaƙar Epstein da Maxwell ba ta daɗe, sun ci gaba da harƙalla na tsawon lokaci.

Bayan an yanke mata hukunci, Maxwell ta ce ta yi da-na-sanin sanin Epstein a ta yi a rayuwarta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bayan an yanke mata hukunci, Maxwell ta ce ta yi da-na-sanin sanin Epstein a ta yi a rayuwarta