...Daga Bakin Mai Ita tare da Auta Baita na Kwana Casa'in

...Daga Bakin Mai Ita tare da Auta Baita na Kwana Casa'in
An wallafa

Daga Bakin Mai Ita, wani shiri ne na BBC Hausa, da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.

A wannan mako, mun kawo muku hira da Musa Muhammad Abdullahi, wanda aka fi sani da suna Auta Baita a cikin shirin Kwana Casa'in na tashar talabijin ta Arewa24.

An haifi tauraron a birnin Zariya da ke cikin jihar Kaduna, ya kuma yi karatun zamani har zuwa matakin babbar difloma.

Ya ce ya fara aikin gwamnati a 1980, a ma'aikatu daban-daban ciki har da ma'aikatar raya al'adu ta jihar Kaduna.

Auta Baita - kamar yadda aka san shi cikin shirin Kwana Casa'in - ya gargaɗi masu fakewa da sana'ar fim suna aikata abin da ya kira ''baɗala".

Ya ce "ɗan fim mai koyar da tarbiyya ne, saɓanin wargaza ta ba".