Abin da yasa babu ginin da ya rushe a garin Hatay na ƙasar Turkiyya

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Abin da yasa babu ginin da ya rushe a garin Hatay na ƙasar Turkiyya
An wallafa

Garin Hatay na da nisan kilomita 100 ne kacal daga wurin da girgizar ƙasar mai karfin maki 7.8 ta farko ta afka wa yankin Syria da Turkiyya.

Gunduma ce a tsakiyar yankin da aka sami rugujewar yawancin gine-gine.

Sai dai yawancin gine-ginen da ke gundumar Hatay na nan daram ba su lalace ba duk da kusancin da yake da shi da yankin da girgizar ƙasar ta fi yin ɓarna..

Ko me yasa haka?