Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Bello

Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Bello
An wallafa

Filin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna ne da Sheikh Muhammadu Bello Abubakar.

An haifi babban malamin na jihar Zamfara ne, a garin Kanwa cikin 1947.

Ya fara karatunsa na allo ne a gidan Liman Muhammadu Sada, Limamin Kanwa.

Farfesa Sani Zahraddeen da Sheikh Nasiru Kabara na cikin malaman da Sheikh Muhammad Bello ya yi karatu a wajensu.

Ku kalli bidiyon domin ji daga bakin malamin.