Yadda cutar cin abinci ke shafar ‘yan mata
Matsalar cin abinci da matasa ke fuskanta, musamman ‘yan mata na iya mummunan tasiri ga yadda jikinsu ke aiki, lamarin da idan yayi kamari ya kan kai ga kwanciya a asibiti, ko kuma asarar rai.
An bayyana kafafen yada zumunta a matsayin wani dandali da ke taimakwa wajen janyo cututtukan cin abinci a tsakanin matasa, musamman ‘yan mata.
Likitocin cututtukan da suka shafi kwakwalwa sun bayyana kasa cutar wadda matsalar kwakwalwa ke janyowa, zuwa kashi biyu.
Matsaloli kamar matsanancin damuwa na daga cikin larurorin da ke janyo yawan cin abinci ko kuma rashin cin abincin, in ji Likita.
Sannan akwai wasu nau’uka biyar na cutar cin abincin, wadanda suke zaman kansu, wato basu da alaka da wata cuta.
Wani binciken da BBC ta yi ya nuna cewa jerin sunayen masu jira don ganin kwarrarun likitoci a kan wannan matsala ta cutar cin abinci ya ninka sau uku a lokacin annobar korona a kasar Ingila.
Wasu alkaluman da ma’aiakatar lafiya ta yankin Ireland Ta Arewa ta fitar sun nuna cewa, masu jiran ganin likita da ke fama da cutar sun karu da kashi 40 cikin dari a shekarar 2020.
Haka zalika wani binciken da aka yi akan walwalar matasa, a yankin a shekarar 2019 ya gano cewa, yaro daya da matashi daya cikin shida da ke yankin na fama da wani nau’i na cutar cin abinci da ke bukatar kulawa a asibiti.