BBC za ta gudanar da muhawara da 'yan takarar Gwamna a Katsina

Bayanan bidiyo, BBC za ta gudanar da muhawara da 'yan takarar Gwamna a Katsina
BBC za ta gudanar da muhawara da 'yan takarar Gwamna a Katsina
An wallafa

A ranar Litinin ne 23 ga watan Janairun 2023 ne BBC za ta gudanar da muhawarar ƴan takarar gwamna a Katsina.

Cikin ƴan takarar da za su yi muhawarar akwai Dikko Umar Radda na Jam'iyyar APC da Garba Yakubu Lado na Jam'iyyar PDP.

Haka kuma akwai Nura Khalil na Jam'iyyar NNPP da kuma Imran Jino na PRP.

Za ku iya kallon wannan muhawara kai tsaye a shafinmu na Facebook BBC Hausa Facebook da YouTube.