Barcelona ba za ta sayar da Frenkie de Jong ba

An wallafa

Barcelona ta ce ba za ta sayar da Frenkie de Jong ba, koda yake Manchester United ta kulla yarjejeniyar daukar dan kwallon.

Kenan Barcelona ta sa shakku a cinikin, watakila tana son a kara mata kudi kan cinikin kafin ta sallama dan kwallon.

A makon jiya United ta amince da farashin fam miliyan 56 da karin tsarabe-tsarabe da Barcelona ta gindaya kan dan kwallon Netherlands.

Sai dai shugaban Barcelona, Joan Laporta ya ce "[De Jong] dan wasan Barca ne har sai munyi niyyar sayar da shi, kuma ba za mu sayar da shi ba.''

De Jong ya koma Barcelona daga Ajax a 2019 kan fam miliyan 65 da karin tsarabe-tsaraben fam miliyan 9.5 kan yarjejeniyar kaka biyar.

BBC Sport ta fahimci cewar har yanzu ana tattaunawa tsakanin kungiyoyin biyu, sai dai Barca tana jan kafa kan bukatar kungiyar da ke buga Premier League.

Idan De Jong ya koma United, zai sake taka leda a karshin koci Erik ten Hag, wanda ya ja ragamar Ajax.

Laporta ya kara da cewar ''Mun kwan da sanin cewar kungiyoyi da yawa na son daukar De Jong, amma yanzu ba za mu sayar da dan kwallon ba.''