Ta wace hanya kamfanin komai-da-ruwanka na TGI ke amfanar manoman Najeriya?

Bayanan bidiyo, Danna hoton sama ku kalli bidiyo
Ta wace hanya kamfanin komai-da-ruwanka na TGI ke amfanar manoman Najeriya?
An wallafa

Kamfanin zuba jari na Tropical General Investments Group a Najeriya (TGI Nigeria) ya ce yana ƙara yawan mu'amalar da yake yi da manoman Najeriya don haɓaka tattalin arzikinsu.

Shugaban kamfaninm, Faruk Gumel, ya faɗa wa BBC cewa an kafa shi ne shekara 40 da suka wuce.

Kamfanin wanda ya mallaki Bankin Union a kwanan nan, ya ce yana ƙara mayard a hankali kan harkokin noma musamman a Jihar Kebbi da ke arewacin ƙasar.