Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Chadi na 2024: Masra da Deby, sabuwar gwamnati ko tazarce
Fafatawar za ta fi zafi tsakanin mai shekara 40 da mai shekara 39 a zaɓen shugaban ƙasar da ke tafe ranar 6 ga watan Mayu.
Ɗayansu na rajin kafa sabuwar gwamnati, yayin da ɗayan ke danganta kansa da jinin tsohon shugaban ƙasar. Shin wane ne zai zama zakara?
Lamari ne da ba a yi tsammanin samu ba, kasancewar Succès Masra, wanda ke riƙon muƙamin firaminista a gwamnatin Mahamat Idriss Deby, ya zama babban abokin karawar Deby a zaɓen da ke tafe.
Samun firaminista da shugaban ƙasa a gwamnati ɗaya su fafata a zaɓe guda abu ne da ba a taɓa yi ba a ƙasar.
Lamarin da masanin siyasar ƙasar, Evariste Ngarlem Toldé ya kira da ''Keɓantaccen lamarin''
Shi kuwa tsohon firaminista a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasar Idriss Deby Itno, Albert Pahémi Padacké, wanda shi ma ke takarar, yana ganin batun kamar share masa hanyar lashe zaɓen, kasancewa manyan jagororin gwamnatin ƙasar sun raba kansu, maimakon haɗa kansu wuri guda.
Hakan na nuna yadda 'yan ƙasar da ma duniya baki-ɗaya suka zaƙu su ga yadda wannan fafatawa za ta kasance.
Tuni dai 'yan takarar suka fara fafatawa da juna ta fatar baki, bayan fara yaƙin neman zaɓe da aka ƙaddamar ranar 14 ga watan Afrilu.
Da alama mutane ba sa tare da mutanen biyu tun watan Afrilun 2021, lokacin da sojoji suka karɓi mulki bayan mutuwar tsohon shugaban ƙasar, Idriss Deby, wanda ya shafe shekara 30 yana kan karagar mulki.
Mista Deby, mai muƙamin Marshal a rundunar sojin ƙasar, ya mutu ne lokacin da ya fuskanci 'yan tawaye a fagen daga da ke arewacin ƙasar.
Mutuwar Idris ta haifar da fatan samun sabuwar gwamnati a Chadi, to sai dai ɗansa Mahamat Deby, ya gaji mahaifinsa nasa a matsayin shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya na soji.
Da farko Mahamat Deby ya alƙawarta mayar da mulki ga gwamnatin dimokraɗiyya cikin wata 18, kafin daga baya ya tsawaita zuwa shekara biyu, bayan wani taron tattauwa na ƙasa.
Bayan kammala taron tattaunawa ta ƙasar da ta bai wa matashin janar ɗin - wanda a lokacin shekarunsa 38 - damar tsayawa takarar, bataun ya haifar da ɓarkewar zanga-zangar a ƙasar, lamarin da ya i sanadin mutuwar mutum fiye da 50 tare da kama fiye da 600.
A watan Fabrairun da ya gabata ne mista Deby ya bai wa al'ummar ƙasar mamaki, ta hanyar bayyana cewa za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasar ranar 6 ga watan Mayu.
Yaya ƙarfin Mahamat Idriss Deby Itno yake?
Ƙarƙashin wata sara da ake kira "12 projects - 100 actions", Mahamat Déby ya gabatar da wani shiri don ƙarƙafa ''zaman lafiya'', da sasanto da tsaro ga al'ummar Chadi.
A ƙarƙashin wannan shirin ɗan tsohon shugaban ƙasar, kuma ɗan takarar jam'iyyar ƙwancen ''United Chad coalition'', ya ɓullo da wasdu tsare-tsare domin gina abin da ya kira ''babbar jamhuriya''.
Mahamat Idriss Deby na iya bakin ƙoƙarinsa wajen fuskantar ƙalubalen da suka danganci matsalar tsaro da zaman lafiya.
Evariste Ngarlem Tolde, wani masanin kimiyyar siyasa a jami'ar Ndjamena, ya ce ba ya ganin kwarewar da shugaban ke da shi a fannin soji za ta taimaka masa wajen ''lashe zaɓen'' .
Mahamat Deby ya ajiye aikin soji, kafin ya gabatar da takardarsa ta sha'awar tsayawa takara a watan Nuwamban bara.
“Nan a fagen siyasa, mutanje ba sa kallon kwarewarka a aikin soji, abin da ka cimma ake la'akari da shi ba kwarewarka a aikin soji ba,'', in ji masanin siyasar.
Kasancewar damuwar da ƙasashen wajen ke dora wa Chadi, ɗaya daga cikin manyan matsalolin da sabuwar gwamnatin ƙasar za ta fuskanta shi ne damuwa kan dangantakar ƙasar da sauran ƙasashen duniya.
“Chadi na kan tsinin matsaloli biyu, wato matsalar masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel da yankin Tafkin Chadi a ɗaya ɓangare, da kuma yaƙin Sudan a gefe guda'', in ji Cameron Hudson wani mai bincike a cibiyar nazarin dabarun yaƙi ta duniya.
Wannan matsala na nuna irin muhimmancin da ƙasar ke da shi wajen shiga a dama da su a tsaron yankin.
Ngarassal Saham Jacques, babban kodinetan hukumar yaƙi da rashawa ta Chadi, OTAC, ya ce duniya ta tabbatar da ƙwarewar Deby a fannin aikin soji.
Dangane da ƙarfin deby a wannan zaɓen, masanin kimiyyar siyasa Ngarlem Toldé, ya ce ''a Afirka, galibi waɗanda suka shirya zaɓe ba su fiya yin rashin nasara ba'', kafin nan kuma, wani abu da ka iya taimaka wa Deby shi ne kasancewarsa ɗan takarar ƙawancen jam'iyyu kusan 227 da ƙungiyoyi fiye da dubu''.
Wanda hakan kuma ya sanya shi a matsayin wande ake ganin na da damar lashe zaɓen.
Me Masra ya dogara da shi?
Success Mara ya gabatar da manufofin jam'iyyarsa ta ƙawancen ''Society of justice and equality”.
Jacques Ngarassal ya ce “abin da Succès Masra ya dogara da shi, shi ne muradin da al'ummar Chadi ke da shi na buƙatar chanji”.
A ganinsa, Masra ya zo da wani batu da matasan ƙasar - waɗanda su ne kaso mafi yawa na masu ƙaɗa ƙuri'a - ke muradi.
A 'yan watanni ƙalilan da ya kwashe a matsayin shugaban gwamnati, ya fara ''tara kudi, tare da ƙulla yarjejeniyoyi, ciki har da wanda zai bayar da dama horas da matasan ƙasar kimanin miliyan guda a manyan jami'o'in Amurka'', wannan na nuna damuwarsa kan ci gaban matasa.
Evariste Ngarlem Toldé ya ce Masra “ya samar da daidaito da adalci da kowane ɗan Chadi ke fatan samu.”
A ganin masanin siyasar, jawabin Masra ya ja hankalin mafi yawan al'ummar ƙasar, inda hakan ke nufin, "ya samu goyon bayan mafi yawan mata da matasan ƙasar."
Remadji Hoinathy, babban mai bincike a cibiyar nazarin tsaro ta djamena, ya yi nazarin Masra a satumban 2022, inda ya bayyana shi da cewa ''wani mutum da ke da manufa.
"Musamman kan matasa waɗanda su ne mafi yawan al'umman Chadi, amma suka kasance mafi ƙarancin rukunin mutanen da suka samu moriyar gwamnati a shekara 30 na gwamnati tsohon shugaban ƙasar Idris Deby.
Ya san yadda zai shirya jawabi da zai janyo hankalin tare da ƙoƙarin haɗa kan al'ummar ƙasar.
Shin akwai maza a gaban Deby?
A ranar 20 ga watan Afrilu ne sojojin ƙasar suka bayyana Mahamat Déby a matsayin shugaban riƙon ƙwaryar ƙasar, inda ya gaji mahaifinsa da ya jagoranci ƙasar na shekara 30.
Al'ummar ƙasar da dama sun yi ta sukar takarasa. Da farko ya alƙawarta miƙa mulki ga farar hula cikin wata 18, to amma daga baya ya ɗage zaɓe zuwa wanan shekara, lamarin da ya yi ta haddasa zanga-zanga da aka zargi jami'an tsaro da musgunawa waɗanda suka shiryata.
Mista Deby ya kuma alƙawarta cewa ba zai tsaya takarar ba, amma daga baya ya sauya matsayarsa.
Ngarlem Tolde ya ce waɗanan alƙawura da Deby ya karya ba za su iya kawo masa wata matsala ba. “Fiye da kashi 90 na al'ummar Chadi marasa ilimi ne. Don haka mutanen ƙasar ba sa la'akari da karya alƙawari,” in ji shi.
Wani ƙarin dama da takarar Mahamat Déby shi ne mutuwar babban abokin hamayyarsa, Yaya Dillo, da ya rasu ranar 28 ga watan Fabrairu bayan wata arangama da sojojin ƙasar a shalkwatar jam'iyyarsa da ke birnin N'Djamena.
Gwamnatin ƙasar ta zargi Dillo da kai hari kan hukumar tsaron ƙasar, zargin ya yi ta musantawa.
Amma Mista Ngarassal, na ganin cewa waɗannan matsalolin sun dusashe farin jinin Mahamat Déby tare da haifar da fargaba game da fatan da ake da shi a kansa.
A matsayinsa na mamba a ƙungiyoyin farar hula na Chadi, Mista Ngarassal ya ce mutuwar Yaya Dillo ka iya haifar da koma baya ga nasarar Mahamat Deby.
“Yaya Dilo babban ɗan hamayya ne. Wannan yanayi ya sa mafi yawan 'yan ƙasar rashin jin dadi. Batu ne da aka jingine har yanzu ba tare da wata matsaya a kansa ba,'' kamar yadda ya bayyana.
Yarjejeniyar Kinshasa ta taimaka wa Masra?
Kasancewar Succès Masra, wanda ɗan hamayya ne a matsayin firaminista ya haifar da suka a cikin jam'iyyun adawa.
Bayan da aka zargi shi da cin amana ta hanyar yin gogayya domin samun nasara a kan Mahamat Déby, Succès Masra na fuskantar zazzafar suka a ƙasar.
“Amincewar da ya yi na zama shugaban gwamnati ya sa mutanen ƙasar da dama na magana a kansa tare da nesanta kansu da shi,'' in ji Ngarlem Toldé.
Komawarsa Chadi ranar 3 ga watan Nuwamban bara, bayan zaman gudun hijira ya aza ayar tambaya kan irin yarjejeniyar da ya ƙulla da gwamnatin Deby.
Da farko, Masra ya tafi zaman gudun hijira ne bayan wata zanga-zanga da 'yan sanda suka murƙushe ta amfani da ƙarfi.
Shekara guda bayan hakan ne ya koma Chadi, bayan shiga tsakani da DR Kongo ta yi, tare da alƙawarin ''ci gaba da tattaunawar siyasar zaman lafiya'',
Ya sanya hannu kan yarjejeniyar sasanci da Mista Deby, kafin a naɗa shi a matsayin firaminista ranar 1 ga watan Janairu.
Dakta Toldé, ya ce yarjejeniyar Kinshasa ka iya haifar masa na raguwar goyon bayan al'umma, yana ganin cewa Masra ''zai iya yin takarar ba tare da yana kan muƙamin firaminista b, ko wani muƙamin gwamnati ba''.
Mista Ngarassal, aɗaya gefen na ganin cewa Masra ya samu damar yin takarar ne ta hanyar yarjejeniyar ta Kinshasa.
Yana mai cewa in da ba don yarjejeniyar ba da Masra ''ba ma zai samu damar komawa Chadi ba, ballanata ya tsaya takara''.
''In da bai karɓi muƙamin firaminsita ba, ba zai samu kariyar da yake buƙata ba wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe,'' in ji shi.
Jam'iyyun hamayya da dama sun nesanta kansu da Succès Masra, domin nuna rashin amincewarsu dangane da afuwar da aka yi duka 'yan Chadi, fararen hula da sojoji, da ke cikin shirin samun afuwar na "Black Thursday".
“Akwai aƙalal jami'yyu 30 da ke hamayya da Mahamat Kaka (Mahamat Idriss Deby) da kuma Masra a ɗaya gefen,” in ji masanin siyasa Ngarlem Toldé.
Wannan rashin “goyon baya” ka iya kawo cikas da sahihancin takararMasra tare da haifar da shakku dangane da aniyarsa ta kawo sauyi a ƙasar.
Baya ga Mahamat Idriss Deby da Succès Masra, akwai sauran 'yan takara takwas da ke fafatawa a zaɓen shugaban ƙasar ciki har da tsohon firaministan ƙasar Albert Pahimi Padacké.
Bayan ƙuri'ar raba-gardamar da ta samar da sabon kundin tsarin mulki, zaɓen na ranar 6 ga watan Mayun zai bai wa ƙasar damar komawa kan tsarin mulkin dimokraɗiyya, tare da kawo ƙarshen gwamnatin riƙon ƙwarya da ake yi a ƙasar tun bayan rasuwar Idriss Déby Itno a 2021.