Haaland ya ci wa City kwallo uku rigis karo na biyu a jere

An wallafa

Manchester City ta sharara kwallo 6-0 a ragar Nottingham Forest a wasan mako na biyar da suka kara ranar Laraba a Etihad.

Erling Haaland ne ya ci uku rigis ta farko a minti na 12 da fara wasa ta biyu a minti na 23 da kuma ta ukun da ya ci saura minti bakwai su je hutu.

Minti biyar da komawa zaaagaye na biyu ne City ta kara na hudu ta hannun Joao Cancelo, sannan Julian Alvarez ya kara biyu a raga.

Haaland ya zama na bakwai da ya ci kwallo uku rigis karo biyu a jere a Premier League, bayan Les Ferdinand da Ian Wright da Thierry Henry da Didier Drogba da Wayne Rooney da kuma Harry Kane.

Haka kuma Haaland ya zama na hudu a irin wannan bajintar a Manchester City a Premier, bayan Aguero da Raheem Sterling da kuma Carlos Tevez.

Kawo yanzu Haaland ya zura tara a raga a wasa biyar da fara Premier League - sabon bajinta da ya kafa, bayan Mick Quinn da Sergio Aguero da kowanne ya zura takwas a raga da fara wasa biyar a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Karo na 32 da Manchester City ta ci kwallo biyar ko fiye da haka a wasa daya a Premier League karkashin Pep Guardiola.

Liverpool ta yi irin wannan bajintar sau 15.