Halin da ilimin 'ya'yan makiyaya ke ciki a Jihar Kuros Riba

Bayanan bidiyo, Halin da ililin 'ya'yan makiyaya ke ciki a wasu sassan Najeriya
Halin da ilimin 'ya'yan makiyaya ke ciki a Jihar Kuros Riba
An wallafa

Akan ce ilimi gishirin zaman duniya, kuma makarantu suna daga cikin manyan hanyoyin samunsa.

Sai dai halin da makarantun 'ya'yan makiyaya ke ciki, yana ci gaba da zama wani babban cikas wajen samar da ilimi mai inganci na addini da na zamani ga 'ya'yan makiyayan a wurare da dama na Najeriya.

AbdusSalam Ibrahim Ahmed ya ziyarci wasu daga cikin makarantun 'ya'yan makiyaya da ke yankin Obudu na jihar Kuros Riba, ga kuma rahoto na musamman da ya hada mana a cikin wannan bidiyon.