Klopp ya nisanta kansa da karɓar aikin kocin Ingila

Jurgen Kloop

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Tsohon kocin Liverpool, Jurgen Klopp, ya nisanta kansa da karɓar aikin kociyan tawagar ƙwallon kafa ta Ingila.

Tun bayan da Gareth Southgate ya ajiye aiki ake ta alakanta dan kasar Jamus da mukamin.

Ingila ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Sifaniya a wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai, wwato Euro 2024 da aka kammala a Jamus a cikin watan Yuli.

Klopp, mai shekaru 57, ya bar Liverpool a karshen kakar da ta wuce yana mai cewa "Ina fama da rashin kuzari" bayan shekaru tara tare da Liverpool.

Kociyan ya lashe Premier League da Champions League da FA Cup da League Cup da Fifa World Club Cup da kuma Uefa Super Cup a Liverpool.

Wanda ya halarci taron koci na kasa da kasa a Wurzburg a Jamus, an tambayi Klopp ko akwai wasu tayin aikin koci da aka yi masa a yanzu haka.

"A halin yanzu babu wata ƙungiya ko tawagar da ta bukaci na yi mata aiki,'' in ji Klopp.

A ranar Talata ne kocin Newcastle United, Eddie Howe, wanda ake alakanta shi da aikin kociyan Ingila, ya ce hukumar kwallon kafar Ingila ba ta tuntuɓe shi kan batun ba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ingila za ta buga wasan farko bayan da Southagate ya bar tawagar, inda za ta fafata da Jamhuriyar Ireland a Nations League ranar 7 ga watan Satumba a Dublin.

Sauran da ake alakanta aikin kocin Ingila har da mai horar da 'yan kasa ƴan kasa da shekara 21 Lee Carsley na Ingila da tsohon kocin Chelsea da Brighton Graham Potter da Thomas Tuchel, wanda ya jagoranci Bayern Munich a baya-bayan nan.

Southgate ya yi murabus bayan Ingila ta sha kashi a gasar Euro 2024 a Jamus, karo na biyu da ya yi rashin nasara a wasan karshe bayan Euro 2021 a Wembley da Italiya ta yi nasara a bugun fenariti.

Klopp wanda ya shafe shekaru bakwai yana horar da Borussia Dortmund kafin ya karbi aikin Liverpool a 2015, ya ce akwai yiwuwar komawa koci a nan gaba.

"Bari mu ga yadda lamarin zai kasance nan da 'yan watanni, babu abin da ke faruwa a halin yanzu," in ji shi.

"Har yanzu ina da sha'awar son yin aikin kociya ƙungiya, domin faranta ran magoya baya da mutane da abokan hulɗa ta ƙwarewata. Bari mu ga abinda zai faru nan gaba."

Klopp ya je Wembley ranar 1 ga watan Yuni a matsayin baƙon Borussia Dortmund a wasan karshe a Champions League, wanda Real Maadrid ta lashe.

Liverpool ta nada kocin Feyenoord, Arne Slot a matsayin wanda ya maye gurbin Klopp.