Hikayata 2024: Labarin Kura a Rumbu

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Hikayata 2024: Labarin Kura a Rumbu
An wallafa

A ci gaba da kawo muku labaran da suka cire tuta a gasar Hikayata ta 2024, a wannan makon mun kawo muku labarin Kura a Rumbu na Amra Awwal Mashi.

Labarin Kura a Rumbu - wanda Amra Awwal Mashi ta rubuta - shi ne ya zo a mataki na biyu a gasar Hikayata ta 2024.

Marubuciyar ta gina labarin nata a kan wata mace da ke yawan hira da maza a shafukan sada zumunta, har wata rana ta faɗa soyayya da ƙasrgumin ɗanbingida da ake nema ruwa a jallo.