Bayern ta fitar da matsaya kan Sane, Inter Milan da Juventus na zawarcin Kiwior

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙungiyar Bayern Munich ta ce ba za ta ƙara wa Leroy Sane kuɗi ba, Napoli ta yi gum game da zawarcin ɗanwasan Manchester City Kevin de Bruyne, sannan Inter Milan da Juventus na gumurzu kan ɗanwasan Arsenal Jakub Kiwior.

Ƙungiyar Bayern Munich ta ce ba za ta ƙara wa Leroy Sane kuɗi ba duk da cewa wakilin ɗanwasan na Jamus ya buƙaci hakan (Florian Plettenberg, Sky Sports Germany).

Daraktan wasanni na ƙungiyar Napoli, Giovanni Manna ya ƙi cewa komai game da yunƙurin ƙungiyar na ɗauko ɗanwasan tsakiya Kevin de Bruyne mai shekara 33 daga Manchester City bayan kwantiraginsa ya ƙare a ƙarshen kakar bana. (Calciomercato).

Ɗanwasan gaban Canada Jonathan David zai bar ƙugiyar Lille ta Faransa a ƙarshen kakar bana, kuma Napoli na zawarcin ɗanƙwallon mai shekara 25.

Shugaban ƙungiyar Bayer Leverkusen, Fernando Carro ya ce akwai yiwuwar ƙungiyar ta ɗauko ɗanwasan Jamus Florian Wirtz, a daidai lokacin da ita ma Bayern Munich ke zawarcinsa. (Sky Sports Germany).

Ƙungiyoyin Juventus da Inter Milan na fafatawa kan ɗanwasan bayan Arsenal, Jakub Kiwior ɗan ƙasar Poland, wanda ke tunanin makomarsa zuwa ƙarshen kakar nan. (Football Insider).

Real Madrid na gab da amincewa da farashin ɗanwasan Liverpool mai shekara 26 Trent Alexander-Arnold na dala miliyan 1 domin ɗaukarsa kafin gasar duniya na ƙungiyoyi. (Football Insider).

Tsohon kocin Everton da Burnley, Sean Dyche na cikin waɗanda ake tunanin za su karɓi ragamar horar da ƙungiyar Leicester City domin maye gurbin kocinta na yanzu Ruud van Nistelrooy wanda ake tunanin za su raba gari. (Talksport)

Ɗanwasan Brazil Douglas Luiz ya ce yana kewar lokacinsa a Aston Villa a yanzu da yake wahalar samun lokacin buga wasa a ƙungiyar Juventus tun bayan zuwansa a kakar bara. (Twitch, via Birmingham Mail).

Brighton ta shiga sahun ƙungiyoyin da suke zawarcin ɗanwasan ƙungiyar Hellas Verona ta Italia, Diego Coppola. (Fabrizio Romano).

AC Milan ta ƙara ƙaimi wajen zawarcin ɗanwasan bayan ƙungiyar Feyernood, David Hancko, a daidai lokacin da ƙungiyoyin Bayer Leverkusen da Juventus suma suke matsa lamba kan ɗan wasan na ƙasar na Slovakia mai shekara 27 (Calciomercato)