Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Rikicin jam'iyyar haɗaka ta ADC da yi wa mutane yankan rago a Zamfara
Kamar kowane mako, wannan maƙala ta duba wasu daga cikin manyan abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da ya gabata.
Me ya janyo rikicin jagoranci a jam'iyyar ADC?
Da alama tun ba aje ko'ina ba rikicin cikin gida ya fara a jam'iyyar haɗaka ta ADC, bayan da tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar ya ce yanzu shi ne jagora mai cikakken iko na jam'iyyar.
Hakan dai na faru ne a daidai lokacin da ƴan jam'iyyar ke iƙararin gujewa rikice-rikicen cikin gida daga jam'iyyunsu na asali da suka baro da suka haɗa da PDP, da APC da LP da kuma NNPP.
Masu fashin baƙi sun sha nanata cewa ita kanta sabuwar tafiyar ba ta tsira ba daga rikicin cikin gida da ke faruwa sakamakon abubuwa da dama da suka haɗa da rashin adalci wurin kasafta jagorancin jam'iyya da ma zarge-zargen da ake yi wa jam'iyya mai mulki na rikita jam'iyyun hamayya.
Me ya faru?
A ranar 2 ga watan Yuli ne dai tsohon shugaban jam'iyyar ADC, kuma wanda ya kafa ta, Ralph Nwosu, ya sanar da rushe jagorancin jam'iyyar domin bai wa sabbin ƴan hamayya da suka shiga jam'iyyar dama.
Karanta cikakken labarin a nan:
Ma'aikatan jinya sun dakatar da yajin aiki
A ranar Juma'a ne ministan lafiya a Najeriya ya ce ma'aikatan jinya da ungozoma ƙarƙashin ƙungiyar National Association of Nigerian Nurses and Midwives (NANNM) sun janye yajin aikin da suka fara yi.
Da yake yi wa manema labarai jawabi, Ali Pate ya ce sun ɗauki matakin janye yajin ne saboda yarjejeniyar da suka cimmma da gwamnatin tarayya bayan wata ganawa a yau ɗin.
A ranar Talata ne ma'aikatan jinyar suka fara yajin aikin saboda abin da ƙungiyar tasu ta bayyana da "gazawar gwamanti wajen biyan buƙatunsu cikin wa'adin kwana 15 da ta bayar" ranar 14 ga watan Yuli.
Akaasrin buƙatun sun jiɓanci walwalar ma'aikata, da alawus-alawus a asibitocin gwamnatin tarayyar Najeriya.
Kashe 'yan Boko Haram tara a jihar Borno
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe mayaƙan Boko Haram tara a jihar Borno da ke area maso gabashin ƙasar.
Dakarun rundunar musamman ta "Operation Hadin Kai" ne suka kashe 'yanbindigar a yankunan kananan hukumomin Konduga, da Bama, da Gwoza.
Bayanai sun ce mayakan sun yi yunƙurin tarwatsa gadar da ta haɗa Marte da Dikwa kafin sojojin su fatattake su, inda suka gano bama-bamai 17 a ƙarƙashin gadar.
Mai magana da yawun rundunar, Kyaftin Reuben Kovangiya, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa an kuma gano makamai, da alburusai, da sauran kayan aiki na mayaƙan.
Ya ce dakarunsu sun yi wa mayakan kwanton bauna bayan yi masu ƙawanya, yayin da a gefe guda kuma jiragen sama ke yi masu luguden wuta, lamarin da ya sa aka kashe tara daga cikinsu.
Daga cikin tarin makaman da akwa ƙwace daga hannun mayaƙan sun haɗa da bindigogi ƙirar AK-47, da kirar PKT a ƙananan hukumomin Konduga, Bama da Gwoza.
Yadda ƴanbindiga suka yi wa mutum 38 yankan rago a Zamfara
Ƴanbindiga sun kashe wasu mutum 38 ta hanyar yi musu yankan rago, daga cikin mutum 56 da suka yi garkuwa da su sakamakon gaza biyan kuɗin fansa da ƴanbindigar suke nema.
Mutanen da aka kashe ɗin sun kasance ƴan ƙauyen Banga da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar ƙauran Namoda da ke jihar Zamfara.
Shugaban ƙaramar hukumar, Manniru Haidara Ƙaura wanda ya shaida wa BBC yadda al'amarin ya faru, ya ce yawancin waɗanda aka yi wa yankan ragon matasa ne.
"Bayanin da muka samu shi ne sun yi musu yankan rago ne. Abin da ya faru shi ne ƴanbindigar sun nemi kuɗin fansa kuma aka harhaɗa aka ba su kamar yadda suka nema, inda kuma suka saki mutum 18 da suka haɗa da mata 17 da ƙaramin yaro guda ɗaya, a ranar Asabar,"in ji Haidara.
INEC za ta fara rajistar masu zaɓe a watan Agusta
Hukumar zaɓen Najeriya ta ce nan gaba cikin wannan wata za ta fara yin rajistar masu zaɓe a faɗin ƙasar gabanin zaɓukan 2027.
Cikin wata sanarwa da INEC ta wallafa a shafinta na X ranar Juma'a, ta ce za ta fara rajistar masu zaɓen ta yanar gizo a ranar 18 gawatn Agustan da muke ciki.
Hukumar zaɓen ta kuma saka ranar Litinin 25 ga watan Agustan a matsayin ranar fara rajistar a ofisoshinta da ke ƙananan hukumomi da sauran wuraren da ta ware don gudanar da aikin.
INEC ta ce za a riƙa gudanar da aikin ne daga ƙarfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana a ranakun Litinin zuwa Juma'a.
Kan hakan ne hukumar ta buƙaci waɗanda ba su da rajistar su yi amfani da damar wajen mallakar rajistar.
Hukumar ta ƙayyade shekara 18 a matsayin mafi ƙanƙantar shekarun yin rajistar zaɓe a Najeriya.
Yadda aka ceto mutum 26 bayan kifewar kwale-kwale a Neja
An yi nasarar ceto mutum 26 a ranar Litinin bayan kifewar wani kwale-kwale a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja da ke arewa maso tsakiyar Najeriya.
Kwale-kwalen na dauke ne da yankasuwa da ke kan hanyar zuwa cin kasuwar Zumba a yankin Kwata a ranar Asabar.
Hukumar agajin gaggawa ta jihar Neja ta ce mutum 13 suka mutu a hatsarin kwale-kwalen da ke dauke da mutum 39.
"Ma'aikatan agaji sun yi nasarar ceto fasinja 26, yayin da aka samu gawar mutum 13 cikin fasinjan da ke cikin kwale-kwalen," in ji Alhaji Abdullahi Baba-Ara, shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar Neja.
Karanta cikakken labarin a nan:
Mamakon ruwan sama ya haifar da ambaliya a Maiduguri
Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno sun tsere daga gidanjensu bayan wata mummunar ambaliya ta auka wa wasu sassan birnin sakamakon ruwan sama mai ƙarfin gaske.
Rahotonni daga birnin sun ce lamarin ya shafi unguwannin Damboa road da Moduganari Ngomari da Bulunkutu Abuja da sauransu.
An dai wayi gari da mamakon ruwan sama a faɗin birnin, lamarin da ya haifar da ambaliyar.
A shekarar da ta gabata ne aka samu wata mummunar ambaliya da ta raba fiye da mutum miliyan guda da muhallansu a birnin na Maiduguri.
Gwamnatin Najeriya ta ce ta samu kuɗin gina titin jirgi daga Maiduguri zuwa Aba
Gwamnatin Najeriya ta ce ta samu duka kuɗin gudanar da aikin gina layin dogo daga birnin Maiduguri na jihar Borno zuwa garin Aba na jihar Abiya.
Ministan Sufuri Saidu Alkali ne ya bayana hakan a yau yayin wani taron bita da ake gudanarwa a Kaduna, kamar yadda wata sanarwa daga ofishinsa ta bayyana.
"Layin dogon mai tsawon kilomita 1,443 zai ratsa jihohin Borno, da Yobe, da Gombe, da Bauchi, da Filato, da Kaduna, da Nasarawa, da Binuwai," in ji sanarwar da kakakin ministan Rabiu Ibrahim ya fitar.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana inda gwamnatin ta samo kudin ba. Akasarin manyan ayyuka masu tsada kamar wannan akan yi su ne ta hanyar bashi ko kuma lamuni.
Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta gyara layin dogo na dakon kaya tsakanin Legas zuwa Kano.