Birtaniya na shirin taƙaita ba da biza ga ƴan wasu ƙasashe

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Birtaniya na shirin taƙaita ba da biza ga 'yan wasu ƙasashe da ake matuƙar zaton cewa za su share wuri su zauna, ko kuma su ce suna neman mafaka, a wani sabon yunƙurin ɗaukar tsattsauran mataki daga gwamnati.

A ƙarƙashin tsare-tsaren Ofishin Harkokin Cikin Gida, wanda jaridar the Times ta fara ruwaitowa, mutanen da suka fito daga ƙasashe kamar Pakistan da Najeriya da kuma Sri Lanka na iya fuskantar ƙarin wahalhalu wajen shiga Birtaniya don yin aiki ko kuma karatu.

Ministoci sun yi imanin cewa akwai wata matsala da ake samu da mutane da suka shiga Birtaniya da bizar yin karatu ko aiki, daga baya suna neman zaman mafaka - wanda idan suka samu, zai ba su damar zama a ƙasar na dindindin.

Wani mai magana da yawun ofishin harkokin cikin gida ya ce: "Tsare-tsarenmu kan shige da fice na gaba za su ɓullo da shirin dawo da doka da oda kan tsarin shige da fice da ya riga ya samu matsala."

Sai dai ba a san ƴan waɗanne ƙasashe ne suka wuce lokacin zama da aka ɗebe musu ba saboda ofishin harkokin cikin gida bai wallafa alkaluman masu ficewa ba tun 2020, sakamakon sake yin duba kan waɗannan alkaluma.

Ba a ɗaukan alkaluman mutane da dama da ke ficewa daga Birtaniya, abin da ke nufin cewa zai iya kasancewa wasu mutanen ba sa ma cikin ƙasar.

Farfesa Jonathan Portes, wani babban jami'i a cibiyar think-tank da ke Birtaniya, ya ce taƙaita ba da bizar ba zai yi wan tasiri mai girma ba kan masu buƙatar neman mafaka.

"Ina tunanin tasirin ba zai shafi mutanen da ke neman zaman mafaka ba, kawai an yi shi ne don rage yawan masu iƙirarin mafaka," kamar yadda ya shaida wa BBC.

"Idan ka samu wanda ke zuwa nan a matsayin ɗalibi sannan ya sauya zuwa mai neman mafaka... wannan cin fuska ne ga tsarin ƙasa - gwamnati na ƙoƙarin rage hakan."

Sabbin alkaluma daga ofishin harkokin cikin gida sun nuna cewa sama da mutum 108,000 suka nemi mafaka a Birtaniya a bara - wanda ba a taɓa samun irin haka ba tun 1979.

Gaba-ɗaya, ƴan Pakistan 10,542 ne suka nemi mafaka a Birtaniya - wanda suka fi na kowace ƙasa. Sri Lanka na da 2,862 sannan Najeriya kuma mutum 2,841.

'Lamarin zai shafi ƴan Najeriya da ba su je da niyya mai kyau ba'

Dakta Mahamud Ahmad Kiru, malami a Jami'ar gabashin birnin Landan da ke Birtaniya, ya ce wannan lamari zai shafi ƴan Najeriya da ke zuwa ƙasar da wata manufa.

"Batun zai shafi ƴan Najeriya da ke son maƙalewa a Birtaniya. Sai dai suna da zaɓi biyu idan matsayin ɗalibai suka je dole ne su mayar da hankali su kammala karatunsu sannan su koma gida.

"Idan kuma suna son su ci gaba da zama dole ne sai sun yi karatu sun yi ƙwazo - sun yi abin da gwamnatin Birtaniya za ta buƙaci ƙwarewarsu. Hakan zai ba su damar su ci gaba da zama a dokance," in ji Dakta Kiru.

Ya ce tsarin gwamnatin ƙasar ya saka tana da duka bayanan kowaye kama daga gidan da mutum yake zaune har ma da bayanansa na banki.

Alkaluma da aka tattara a 2023 zuwa 2024 sun nuna cewa akwai ɗalibai 732,285 daga ƙasashe daban-daban a Birtaniya, inda 107,480 suka fito daga Indiya sannan 98,400 kuma daga China.

Masu neman bizar aiki ko karatu a Birtaniya ya ragu a 2024, idan aka kwatanta da shekara ta 2023.

Tun bayan zama Firaiminista a bara, Sir Keir Starmer ya yi alkawarin rage yawan mutane da ke shiga ƙasar ba bisa ka'ida ba har ma da waɗanda ke shiga ta hanyar da ta dace - sai dai bai ba da alkaluman da ake son rage wa ba.

Tsare-tsaren jam'iyyar Labour na rage yawan bakin-haure sun haɗa da idan aka saka rayuwar mutane cikin haɗari a bakin teku ya zama babban laifi, da kuma taƙaita ƙananan jiragen ruwa daga tsallakar da bakin-haure.

Sir Keir ya soki gwamnatin Conservative da ta gabata, inda ya ce sun ƙasa taƙaita yawan bakin-haure da ke shiga ƙasar.

Yawan bakin haure da ke shiga Birtaniya da kuma waɗanda ke barin ƙasar ya kai 906,000 a watan Yunin 2023, sannan ya yi ƙasa zuwa 728,000 a shekarar zuwa tana Yunin 2024.

Sabbin matakai da tsohon Firaiminista Rishi Sunak ya ɓullo da su da nufin rage bakin haure, sun taimaka wajen rage yawansu.

Gwamnatin Conservative da ta gabata ta ƙara albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikatan ƙasashen waje da ke son zuwa aiki Birtaniya daga fam 26,200 zuwa fam 38,700 - ta kuma haramta wa ma'aikatan gidajen reno kai iyalansu ƙasar.

A lokacin jam'iyyar Labour na cikin matsin lambar yin sauye-sauye kan tsarin shige da fice - sai dai matsin lambar ta ƙaru bayan nasarar da jam'iyyar Reform ta samu a zaɓukan ƙananan gundumomi a makon da ya gabata.

Reform ta lashe kujeru 677 cikin 1,600 da aka fafata ranar Alhamis.

A cikin alkawuranta lokacin yaƙin neman zaɓe, Reform ta ce za ta dakatar da shige da ficen da ba shi da muhimmanci. Za a bar waɗanda ke da ƙwarewa - misali a fannin kiwon lafiya - su shiga Burtaniya.

Da yake mayar da martani game da sakamakon zaɓen a makon da ya gabata, Sir Keir ya ce rashin nasara da jam'iyyarsa ta yi zai zaburar da shi wajen cika ɗaukacin alkawuran da suka ɗauka musamman ma na shige da fice da ayyukan jama'a.

Babban jami'in hukumar kula da ƴan gudun hijira, Enver Solomon ya ce "wasu mutanen da ke aiki ko neman biza na iya samun rayuwarsu cikin haɗari saboda yanayin siyasa a ƙasarsu ya canza", ya ƙara da cewa daidai ne "a kare su daga cutarwa kuma a saurari buƙatarsu a tsarin neman mafaka".

Tuni aka fara aiwatar da shirye-shiryen magance matsalar masu tsawaita zama a ƙasar kafin zaen ƙananan hukumomi.

Ana sa ran za a wallafa cikakken bayanan tsare-tsaren gwamnati kan bakin haure a cikin watan Mayu.

Mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida ya ce: "Don magance cin fuska daga ƴan ƙasashen waje da ke zuwa kan bizar aiki da kuma karatun sannan su ɓige da neman mafaka, muna tattara bayanan sirri kan waɗannan mutane don gano su da wuri da kuma sauri.

"Muna ci gaba da sabunta tsarin biza a koyaushe kuma za mu gano abubuwan da ke faruwa, wanda zai iya lalata dokokin shige da ficenmu, ba za mu yi shakkar ɗaukar mataki ba.

"A karkashin shirin mu na yin sauyi, sabon tsarin mu na shige da fice zai ɓullo da shirin na mayar da doka da oda ga tsarin wanda ke fuskantar matsala."