'Yan wasan Najeriya da za su kara da Guinea gida da waje

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar kwallon kafa ta Najeriya za ta kara da ta Guinea Bissau a wasan neman shiga gasar kofin Afirka a Abuja ranar Juma'a.
Tun ranar 19 ga watan Maris 'yan wasan da Super Eagles ta gayyata suka isa sansanin tawagar, domin atisayen tunkarar karawar gida da waje.
Cikin wadanda Jose Santos Peseiro ya gayyata har da kyaftin Ahmed Musa da Victor Osimhen da Ademola Lukman da karin wasu 20.
Najeriya za ta fara kece raini ranar Juma'a a filin wasa na Moshood Abiola a Abuja da yammaci, sannan su buga wasa na biyu ranar 27 ga watan Maris a Bissau.
Super Eagles ce ta daya a rukunin farko da maki shida, bayan da ta doke Saliyo da Sao Tome, ita kuwa Bissau tana ta biyu da maki hudu, bayan doke Sao Tome da canjaras da Saliyo.
Alkalin wasa shine Mahmoud Elbana, wanda zai yi aiki tare da Youssef Elbosaty da Sami Halhal da kuma Ahmed El-Ghandour, dukkansu daga Masar.
Kwamishinan karawar shine Prosper Harrison Addo daga Ghana, yayin Kotey Alexander zai auna kwazon alkalan wasan ranar Juma'a.
Jerin 'yan wasan Super Eagles:
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masu tsaron raga: Francis Uzoho (AC Omonia, Cyprus); Victor Sochima (Rivers United); Kingsley Aniagboso (Giant Brillars)
Masu tsaron baya: Oluwasemilogo Ajayi (West Bromwich Albion, England); Bright Osayi-Samuel (Fenerbahce SK, Turkey); Kevin Akpoguma (TSG Hoffenheim, Germany); Kenneth Omeruo (CD Leganes, Spain); Calvin Bassey (FC Ajax, The Netherlands); Daniel Bameyi (YumYum FC); Zaidu Sanusi (FC Porto, Portugal); Bruno Onyemaechi (Boavista FC, Portugal)
Masu buga tsakiya: Wilfred Ndidi (Leicester City, England); Frank Onyeka (Brentford FC, England); Alex Iwobi (Everton FC, England); Joe Aribo (Southampton, England)
Masu cin kwallaye: Kelechi Iheanacho (Leicester City, England); Ahmed Musa (Sivasspor K, Turkey); Samuel Chukwueze (Villarreal CF, Spain); Moses Simon (FC Nantes, France); Ademola Lookman (Atalanta BC, Italy); Terem Moffi (OGC Nice, France); Victor Osimhen (Napoli FC, Italy); Paul Onuachu (Southampton FC, England)











